Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Karshe Ta Neman Tsige Gwamnan PDP, Ta Ba da Bahasi
- A yau Talata ce 9 ga watan Janairu Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta duba shari'ar zaben gwamnan jihar Delta
- Kotun ta tanadi hukunci kan shari'ar da ake yi tsakanin PDP mai mulki da kuma APC da LP da kuma SDP
- A kwanakin baya, Kotun Daukaka Kara da ke Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori a matsayin gwamnan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Delta, Punch ta tattaro.
Kotun ta tanadi hukuncin ne yayin da dan takarar jam'iyyar APC a zaben, Ovie Omo-Agege ya shigar da korafi kan zaben.
Wane hukunci kotun ta yanke a baya?
Har ila yau, dan takarar jam'iyyar LP, Ken Pele da na jam'iyyar SDP, Kenneth Gbaji sun kalubalanci zaben da aka gudanar a watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kwanakin baya, Kotun Daukaka Kara da ke Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori a matsayin gwamnan jihar.
Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen 'yan takarar sauran jam'iyyun guda uku saboda rashin gamsassun hujjoji, cewar Channels TV.
Yawan kuri'un da ko wane dan takara ya samu a zabe
Oborevwori na PDP ya samu kuri'u 360,234 yayin da mai bi masa, Ovie Omo-Agege na APC ya samu kuri'u 240,229 a zaben.
Yayin da Ken Pela na LP ya samu kuri'u 48,027 sai kuma dan takarar jam'iyyar APGA, Great Ogboru ya samu kuri'u 11,021 a zaben, The Nation ta tattaro.
Kotun Koli ta tanadi hukunci kan zaben Ebonyi
A wani labarin, Kotun Koli a jiya Litinin 8 ga watan Janairu ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Ebonyi.
A baya Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru na jami'yyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.
Har ila yau, kotun ta yi watsi da korafin dan takarar jam'iyyar PDP, Chukwuma Odili da kuma jami'yyarsa saboda rashin gamsassun hujjoji.
Asali: Legit.ng