Rikici Ya Kaure: An Yi Karar Ministan Buhari a Kotu Saboda 'Wargaza' Jam’iyyar APC
- Shugabannin APC na reshen jihar Osun ba su daina fada da mutanen Ogbeni Rauf Aregbesola ba
- Mataimakin sakataren jam’iyyar APC ya yi hayar lauya, an shigar da kara a kan kungiyar Omoluabi
- Ayodele Kusamotu ya fadawa kotun tarayya da ke Osogbo, Omoluabi ‘yan taware ne a jam’iyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Osun - Jam’iyyar APC mai mulki ta reshen jihar Osun ta shigar da karar Rauf Aregbesola a babban kotun tarayya da ke garin Osogbo.
APC ta yi karar tsohon gwamnan ne bisa zargin kawo rabuwar kai a jam’iyya mai-ci a Najeriya, Premium Times ta fitar da rahoton nan a jiya.
Mataimakin sakataren APC a jihar Osun, Waheed Adeniran ya shigar da kara ta hannun wani lauyan jam’iyyar, Ayodele Kusamotu esq.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayodele Kusamotu esq. ya bukaci kotun tarayyar ta ayyana kungiyar Omoluabi da aka kafa a matsayin ‘yan taware cikin jam’iyyar APC.
APC tayi karar 'yan Rauf Aregbesola
Daga cikin wadanda aka hada a karar mai lamba FHC/OS/CS/1/2024, akwai hukumar zabe ta INEC da wasu daga cikin yaran Rauf Aregbesola.
Ragowar wadanda za su kare kan su a kotu su ne tsohon ‘dan majalisar tarayya, Rasheed Afolabi da tsohon Kwamishina, Lani Baderinwa.
APC ta reshen jihar Osun ta na so a daina alakanta 'yan kungiyar Omoluabi da ‘ya ‘yanta da jam’iyyarsu kuma a ci su tarar Naira miliyan 5.
Rokon jam'iyyar APC a kotun tarayya a Osogbo
Leadership ta ce Kusamotu ya roki alkali ya haramta aikin kungiyar Omoluabi Progressives (APC) kuma a hana ta amfani da tambarin APC.
Idan lauyan da ya shigar da karar ya dace, za a haramtawa ‘yan tawaren aiki da tambari, take da duk wasu alamomi da jam’iyya mai-ci.
Mutanen Aregbesola a APC ba su san ana yi ba
Da Punch ta tuntubi Lowo Adebiyi, ya nuna bai san an shigar da kara a kan Omoluabi ba wanda aka dade ana yin rikici da su a jam'iyyar APC.
Tsohon kwamishinan yada labaran na gwamnatin Aregbesola ya ce su ba ‘yan taware ba ne, ya ce su kungiyar halatattun iyayen APC ne.
Jam'iyyar APC da siyasar Kano
Magoya bayan APC sun sa rai za su koma gidan gwamnati a jihar Kano idan Nasiru Yusuf Gawuna ya yi nasara a kan NNPP a gaban kotun koli.
APC ta fara raba kayan da za ayi amfani da su a ranar rantsar da Nasiru Gawuna.
Asali: Legit.ng