Jerin Kararraki 21 da Kotun Koli Zata Saurara da Yanke Hukunci Kan Zaben Wasu Gwamnoni a Mako 1

Jerin Kararraki 21 da Kotun Koli Zata Saurara da Yanke Hukunci Kan Zaben Wasu Gwamnoni a Mako 1

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - A wannan makon ne ake sa ran kotun koli za ta saurari kararraki 21 da suka taso daga takaddamar zaben gwamna da aka yi ranar 18 ga Maris, 2023 a Najeriya.

A cikin jadawalin da ta tsara na wannan mako, kotun za ta saurari kararrakin jihohin Ebonyi, Filato, Delta, Adamawa, Abia, Ogun, Kuros Riba da Akwa Ibom daga yau zuwa Alhamis.

Kotun kolin Najeriya.
Kararraki 21 da Kotun Koli zata zauna a kai kan zaben gwamnoni a wannan makon Hoto: Supreme Court
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta gano cewa kotun koli mai daraja ta ɗaya za ta iya yanke hukunci a kararrakin zaben gwamnan jihar Kano da Legas da sauran su ranar Juma'a.

Vangaurd ta ce a jadawalin tsare-tsaren kotun wacce ake wa taken daga ke sai Allah ya isa na wannan makon da muka shiga yau Litinin, zata saurari ƙorafe-ƙorafe kamar haka:

Kara karanta wannan

Cikakken jerin gwamnonin jihohi 4 da za su san makomarsu a Kotun Koli a makon nan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihar Ebonyi

Dangane da zaben gwamnan Ebonyi, kotun koli ta shirya sauraron ƙarar da ɗan takarar APGA, Odoh Benard; ya ɗaukaka zuwa gabanta da kuma korafi biyu na ɗan takarar PDP, Chukwuma Odii Ifeanyi a yau Litinin

Jihar Benuwai

Haka nan a yau Litinin, kotun ta tsara zama kan kararraki biyu da ɗan takatar PDP a zaben gwamnan jihar Benuwai, Uba Titus, ya ɗaukaka yana tuhumar APC, INEC da wasu.

Jihar Filato

A ranar Talata, 9 ga watan Janairu, 2024, kotun koli ta tsara sauraron ƙorafi uku da gwamnan jihar Filato kuma ɗan takarar PDP, Celeb Mutfwang, ya ɗaukaka kan tsige shi da kotun ɗaukaka ƙara ta yi.

Jihar Delta

A wannan rana ta Talata (gobe) kotun zata kasa kunne ta saurari kararaki uku da ƴan takara uku, Kenneth Gbagi na SDP, Ovie Omo-Agege na APC da Peta Kennedy na LP suka ƙalubalanci zaben gwamnan Delta.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

Jihar Adamawa

Idan Allah ya kaimu ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, kotun ƙoli ta shirya zama kan ƙararraki biyu da suka shafi zaben gwamnan Adamawa da ƙara ɗaya da Gwamna Fintiri ya shigar.

Jihar Abiya

Sauran kararrakin biyu da kotun zata zauna kansu ranar Laraba, Okechukwu Ahiwe na PDP da Ikechi Emenike na APC ne suka shigar da su kan zaben gwamnan jihar Abia.

Jihar Ogun

A ranar Alhamis, kotu na shirin sauraron kararraki biyu kan zaɓen jihar Ogun waɗanda Oladipo Adebutu na PDP ya shigar da karar Adedapo Abiodun na APC (gwamnan).

Jihar Kuros Riba

Bugu da ƙari, kotun kolin zata saurari ƙara ɗaya tilo da ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP, Farfesa Sandy Onor, ya shigar kan zaben jihar Kuros Riba ranar Alhamis.

Akwa Ibom

Duk a wannan rana ta Alhamis, 11 ga watan Janairu, kotun zata zauna kan karar ɗan takarar gwamnan YPP a Akwa Ibom, Akpan Udofia, da ƙarar takwaransa na NNPP, John Akpan Udoedehe.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar neman tsige gwamnan APC, ta fadi dalilai

Ɗan takarar APC a Filato ya miƙa buƙata ga kotun koli

A wani rahoton kuma Ɗan takarar gwamnan APC a jihar Plateau, Nentawe Yilwatda, ya buƙaci kotun ƙoli da ta yi watsi da buƙatar Gwamna Caleb Mutfwang.

Nentawe ya buƙaci kotun da ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka wanda ya ba shi nasara a zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262