Ganduje Ya Bayyana Gwamnoni, Sanatoci Da Yan Majalisar Da Za Su Dawo APC

Ganduje Ya Bayyana Gwamnoni, Sanatoci Da Yan Majalisar Da Za Su Dawo APC

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam'iyyar nan va da jimawa ba za ta ƙara samun sabbin mambobi
  • Ganduje ya yi nuni da cewa gwamnoni, sanatoci da ƴan majalisu na jam'iyyun adawa na kan hanyarsu ta sauya sheƙa zuwa APC
  • Shugaban na APC ya kuma yi nuni da cewa jam'iyyar ta shirya samun nasara a zaɓukan cike gurbi dake tafe a watan Fabrairu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnonin jihohi da ƴan majalisar tarayya daga jam’iyyun adawa na kan hanyarsu ta zuwa jam’iyyar mai mulki.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kuma ce jam’iyyar APC ta shirya tsaf domin ci gaba da samun nasarar lashe dukkan kujerun da za a yi zaɓen cike gurbi na watan Fabrairu a faɗin ƙasar nan, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Jigon LP ya magantu kan yiwuwar hadewar Atiku, Kwankwaso da Peter Obi

Ganduje ya magantu kan shirye-shiryen APC
Ganduje ya yi nuni da cewa jam'iyyar APC za ta samu sabbin mambobi nan ba da jimawa ba Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Ya bayyana haka ne a garin Lafia babban birnin jihar Nasarawa yayin da ya karɓi wani jigo a jam’iyyar PDP Sanata Solomon Ewuga zuwa jam’iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokaci guda kuma, jam’iyyar APC ta zaɓo ƴan takararta na zaɓen cike gurbi a Ebonyi, Legas, Taraba da sauransu.

Ganduje ya faɗi shirin da APC ke yi

A cewar Ganduje jam’iyyar mai mulki ta ƙuduri aniyar zurfafa da faɗaɗa dimokuraɗiyya a Najeriya.

Dangane da haka, ya ce jam’iyyar tana da “tsarin tabbatar da cewa mun samu ƙarin gwamnoni, Sanatoci da ƴan majalisar wakilai.”

Ya cigaba da cewa:

"Na yi matuƙar farin ciki da a nan jihar Nasarawa mun cimma burinmu na farko ta hanyar rungumar mutane daga jam’iyyun siyasa daban-daban. Muna matukar farin ciki cewa APC ita ce babbar jam’iyyar siyasa a Afirika da ke aiki da ƙabilu daban-daban, masu bambancin addini."

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta barke tsakanin jam'iyyar APC da gwamnanta kan abu 1

Rigima Ta Kunno Kai Tsakanin Gwamna Alia da APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sabuwar rigima ta kunno kai a tsakanin Gwamna Hyacinth Alia da jam'iyyar APC a jihar Benue.

Hakan ya samo asali ne bayan gwamnan ya dakatar da zaɓen fidda gwani wanda jam'iyyar ta shirya gudanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng