Dar-Dar Yayin Da Ake Sauraron Hukuncin Kotun Koli a Shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Kano

Dar-Dar Yayin Da Ake Sauraron Hukuncin Kotun Koli a Shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Kano

  • Mutanen jihar Kano tun daga malamai, ‘yan siyasa da sauran al’umma su na jiran hukuncin kotun koli
  • Shari’ar zaben gwamna tsakanin APC da Abba Kabir Yusuf za ta kare ne kwanan nan a babban kotun kasar
  • Karamin kotun da na daukaka kara sun tsige gwamnatin Abba Kabir Yusuf, aka tabbatar da nasara ga APC

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Masu ruwa da tsaki a jam’iyyu da magoya baya da sauran jama’a na sauraron hukuncin karshe a shari’o’in zaben gwamnoni.

Inda abin ya fi jan hankali shi ne jihar Kano, ana tsammanin kotun koli ta tsaida ranar yanke hukunci a shari’ar zabe a Junairun nan.

Abba Kabir Yusuf, Nasir Yusuf Gawuna
Gwamnan Jihar Kano da 'Dan takaran APC Hoto: Abba Kabir Yusuf, Nasir Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

'Yan NNPP da Kwankwasiyya na zanga-zanga

Magoya bayan jam’iyyar NNPP suna ta yin taron addu’o’i da zanga-zanga a fadin kasar domin yin Allah-wadai da hukuncin alkalan.

Kara karanta wannan

Daliban Najeriya 15, 000 sun yi carko-carko da aka dakatar da karbar digirin Benin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ‘yan sanda, Muhammad Hussein Gumel ya haramta zanga-zangar, har an kama wasu matasa da su ka sabawa wannan doka.

Ana gardamar wanda ya ci zaben Kano

Jagora a APC, Alhaji Alhassan Yaryasa, ya fadawa jaridar cewa mabiyan NNPP da Kwankwasiyya ya kamata da laifin bijirewa umarnin.

Alhassan Yaryasa ya ce ‘yan NNPP suna zanga-zanga ne domin neman goyon bayan jama’a domin tun farko ba su ci zaben gwamna ba.

An nemi jin ta bakin shugaban NNPP na Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ba a dace ba yayin da malaman musulunci ke ta kiran ayi adalci.

Kano: NNPP, Abba sun tafi kotun koli

Lauyoyin NNPP, Abba Kabir Yusuf da INEC sun daukaka kara a kotun koli bayan an samu rudani a kan hukuncin kotun daukaka kara.

A zaman sauraron shari’ar da aka yi a a watan Disamban 2023, kotun kolin ta gamsu kotun daukaka kara tayi kuskure a takardun CTC.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya samu gagarumin goyon baya yayin da Kotun Koli ke dab da yanke hukunci

Punch ta ce sauran jihohin da shari’ar zaben gwamnonin 2023 ta je kotun sun hada da Legas, Ogun, Nasarawa, Bauchi da kuma Filato.

A jihohi Ogun da Filato, PDP da APC duk sun bugi kirji suna sa ran yin nasara a kotun koli.

Shekarau: Abba ko Gawuna?

Kwanaki aka rahoto Malam Ibrahim Shekarau ya fadawa Abba Kabir Yusuf, Nasiru Gawuna da mutanen Kano su roki zabi mafi alheri.

Tsohon gwamnan na Kano ya ce a shari’ar zaben gwamna da ke kotun koli, ya kamata a bar zabi ne ga Ubangiji madaukakin Sarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng