Kotun Koli: Jerin Manyan Shari’ar Zaben Jihohi 4 a Arewa da Za Su Dauki Hankali a 2024
- Ba shakka za a sha kallo a Kotun Koli a 2024, inda ake jiran hukuncin da kotun za ta yanke kan shari'o'in jihohin Arewa
- Akalla jihohi hudu ne shari'ar gwamnan su ta fi daukar hankali, la'akari da tataburzar da aka sha a shari'o'in a 2023
- Kano, Zamfara, Filato da Nasarawa, su ne jihohin da Legit Hausa za ta yi fashin baki kan su, don fahimtar inda aka dosa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
A shekarar da ta gabata, kotunan shari'a a Najeriya sun cika da shari'o'in da suka shafi zaben 2023, yayin da wasu aka kai karshe, wasu na a Kotun Koli a yanzu.
Shari'o'in zaben gwamnan Kano, Filato, Nasarawa da Zamfara su ne manyan shari'o'i yanzu, kuma 'yan Najeriya sun zura idanuwa su ga abin da zai faru.
Ga wani bayani daki daki kan manyan shari'o'in zabe da za su dauki hankali a Kotun Koli a wannan shekarar, kamar yadda shafin Business Day ya tattara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shari'ar zaben gwamnan Kano
Hukumar INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf matsayin gwamnan Kano a zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023, sai dai APC ba ta yarda da sakamakon ba.
Kotun kararrakin zabe ta jihar Kano, ta tsige Gwamna Abba daga kujerarsa, saboda wasu lalatattun kuri'u da kotun tace NNPP ta yi amfani da su, rahoton Daily Trust.
Haka ma kotun Daukaka Kara, ta kori Abba, tare da ba Nasiru Gawuna na APC nasara, inda shi kuma Abba ya garzaya Kotun Koli.
Kotun Koli a zamanta ba farko kan shari'ar, ta saurari kowanne bangare, amma ba ya yanke hukunci ba, ta dage zaman kotun zuwa wani lokaci.
Shari'ar zaben gwamnan Filato
A zaben gwamnan Filato kuwa, Caleb Mutfwang na PDP ya samu kuri'u 525,299, yayin da Nentawe Goshwe na APC ya samu kuri'u 481,370.
Goshwe ya shigar da kara kotun zaben jihar, amma ta ba Mutfwang nasara, sai dai Kotun Daukaka Kara ta yarda da korafin Goshwe, ta tsige Mutfwang daga gwamnan Filato.
Tuni gwamnan ya garzaya Kotun Koli don kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Karar, inda ya ke fatan za a yi masa adalci.
Shari'ar zaben gwamnan Nasarawa
David Ombugadu na jam'iyyar PDP ya kalubalanci nasarar Abdullahi Sule na APC bayan lashe zaben jihar, inda ya ce shi ne ya fi samun kuri'u mafi rinjaye.
A watan Oktoba, kotun zaben jihar ta ayyana Ombugadu matsayin wanda ya lashe zaben, amma Kotun Daukaka Kara ta ce Sule ne ya ci zabe ba Ombugadu ba.
Dukan su dai yanzu suna gaban Kotun Koli, inda shi ɗan takarar PDP ya kalubalanci hukuncin Kotun Daukaka Karar.
Shari'ar zaben gwamnan Zamfara
A zaben watan Maris na 2023 ne INEC ta ayyana Dauda Lawal na PDP matsayin wanda ya lashe zaben jihar Zamfara, inda ya lallasa gwamna mai ci Bello Matawalle.
Sai dai Matawalle da jam'iyyar APC ba su yarda da sakamakon zaben ba, suka tafi kotun zaben jihar, inda ita ma kotun ta tabbatar da nasarar zaben Lawal.
Duk da haka, Matawalle da APC suka garzaya Kotun Daukaka Kara, inda ta ba su nasara, lamarin da ya da Lawal da PDP suka daukaka kara zuwa Kotun Koli.
"Kai jan gwarzo ne": Tinubu ya jinjinawa Abba Gida-Gida
A wani labarin kuma, shugaban kasa Bola Tinubu ya taya gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf murnar cika shekara 61 a duniya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis dauke da sa hannun Chief Ajuri Ngelale, Tinubu ya ce Gwamna Yusuf ya yi gwagwarmaya har ya zama gwamnan Kano.
Asali: Legit.ng