Dalilin Da Ya Sa Ya Kamata Atiku Ya Hakura Da Takarar Shugaban Kasa, Deji Adeyanju
- Deji Adeyanju, wani mai rajin kare hakkin dan Adam, ya shawarci Atiku Abubakar da ya hakura da yin takarar shugaban kasa a 2027
- A cewar Adeyanju, Atiku na da girman kai, rashin iya mu'amala da mutane da sauran matsalolin da ke tasiri a harkar siyasarsa
- Ya tariyo yadda tsohon mataimakin shugaban kasar ya ki hada hadu da wasu manyan 'yan siyasa, wadanda a karshe suka koma bayan Tinubu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wani mai rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju ya fadi dalilan da ya sa ya kamata Atiku Abubakar ya yi murabus daga harkokin siyasa gaba daya.
A cewar Deji Adeyanju, girman kai, rashin iya mu'amala, rashin dattako da sauran dalilan su ka ja Atiku ya fadi zaben 2023.
Dalilin faduwar Atiku zaben 2023
Adeyanju ya bayyana hakan a sakon murnar sabuwar shekarar da ya fitar, inda ya ce da Atiku ya yi abin da ya dace a jam'iyyar PDP, da ya ci zaben shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai rajin kare hakkin dan Adam din ya kuma kalubalanci Atiku kan gaza hada hannu da Peter Obi, Rabiu Kwankwaso da Nyesom Wike a zaben da ya gabata, rahoton Leadership.
Ya kuma ce ire iren mutanen da ya lissafa da kuma kungiyar gwamnoni ta G5, su ne suka share hanyar da Tinubu ya bi ya zama shugaban kasa, cewar rahoton The Punch.
A karshe Adeyanju ya ce ya kamata Atiku ya dauki kaddarar da Allah ya dora masa, ya hakura da yin takara a babban zaben 2027 don ba masu jini a jika damar fafatawa.
Yadda jam'iyyun adawa za su kwace mulki hannun Tinubu a 2027
Wani jigon jam'iyyar PDP, Daniel Bwala ya ce jam'iyyun adawa za su iya kwace mulki hannun jam'iyyar APC a zaben 2017 idan har suka hada kansu.
Idan kuma jam'iyyun suka gaza hada kansu, Bwala ya ce Shugaba Tinubu zai yi shekara takwas ba tare da samun turjiya ba.
Asali: Legit.ng