Shugaban IOTB Ya Faɗa Wa Tinubu Wurin da Zai Ga Maganin Matsalolin Najeriya a Alqur'ani Mai Girma
- An shawarci Bola Ahmed Tinubu ya koma cikin Alqur'ani mai girma akwai maganin dukkan matsalolin Najeriya
- Farfesa Abdullahi El-Okene, shugaban ƙungiyar IOTB ne ya aike da saƙo ga shugaban ƙasa a wurin wani taro a Abuja
- Ya ce babu ta yadda wani ɗan adam zai iya magance halin da Najeriya ke ciki dole sai an nemi taimakon Allah SWT
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kungiyar ‘yan uwa Tijjaniyyah ta duniya (IOTB), Farfesa Abdullahi El-Okene, ya bada shawarin yadda za a magance matsalolin da suka dabaibaye ƙasar nan.
Malamin Musuluncin ya bukaci ‘yan Najeriya da su nemi taimakon Allah wajen ganin an magance dimbin kalubalen da kasar ke fama da su, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
El-Okene, wanda ya bayyana hakan a yayin taron kungiyar IOTB da kungiyar ɗalibai Musulmi ta Darikar Tijjaniyya ta Najeriya karo na 13 a ranar Talata a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganin matsalar Najeriya na cikin Alƙur'ani mai girma
Shehin Malamin bukaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya nemo hanyoyin magance matsalolin taɓarɓarewar tattalin arzikin Najeriya a cikin Alkur’ani mai girma.
Farfesa El-Okene ya roƙi al’ummar musulmi musamman shugabanni da su nisanci hanyoyin da ba su da tushe daga Allah, komai burgewar da suke da shi.
Ya yi kira ga malaman addinin Musulunci musamman mabiya ɗarikar Tijjaniyya ds su dage wajen yi wa al'umma nasiha kan aiki na gari da Allah ke so, su guji ayyukan saɓo.
A cewar Abdullahi El-Okene, ta hanyar ɗa'a ga Allah da kuma kaucewa ayyukan da ya haramta ne zai kawo wa al'umma agaji a dukkan halin da suka tsinci kansu.
Abubuwan da aka yi a taron sun haɗa da wayar da kan jama'a game da aikin jinya a gidajen ƴan gudun hijira da ke Durmi a birnin tarayya Abuja.
Haka nan kuma an bada horo na musamman ga mahalarta taron kan abubuwa da dama.
Wani matashin malami a Ɗanja, Malam Abdullahi, ya shaida wa Legit Hausa cewa malamai sun daɗe suna faɗa wa shugabanni haka amma ba zasu ɗauka ba.
"Ai bari na taƙaice maka, duk wata jarabawa da musiba kowace iri ce akwai hanyar warware ta a Musulunci. To matsalar shi ne ba za a yi aiki da Alƙur'ani ba a Najeriya.
"Malamai sun jima suna faɗin cewa a koma ga Allah, mutane su gyara tsakanin su da Ubangiji, amma ba a ɗauki maganarsu da muhimmanci ba."
Malam Abdullahi ya ƙara da cewa duk wata jarabawa da al'umma suka shiga, zaka ga wani laifi ne da wasunsu ke aikatawa sai Allah ya jarabce su.
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sake Motsi Mai Girma a Jihar Kano
A wani rahoton na daban Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shaida bikin rantsar da manyan sakatarori 11 tare da sabbin masu bada shawara ta musamman 14.
Ya yi wannan ne yayin da ake ci gaba da dakon zaman karshe na yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano a kotun koli.
Asali: Legit.ng