Bayan Ya Samu Babbar Matsala, Gwamnan PDP Ya Yi Magana Kan Hakura da Mukaminsa

Bayan Ya Samu Babbar Matsala, Gwamnan PDP Ya Yi Magana Kan Hakura da Mukaminsa

  • Gwamna Siminilayi Fubara na jihar Rivers ya caccaki masu adawa da shi kan rikicin siyasar jihar
  • Fubara ya sha alwashin ba zai taɓa miƙa ragamar mulki ga masu fafutukar ganin sun kore shi daga muƙaminsa ba
  • Tsofaffin abokan ƙawancen, Wike da Fubara, sun yi takun-saka kan yadda ake tafiyar da tsarin siyasar jihar Rivers

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminilayi Fubara, ya ba da tabbacin cewa babu wani rikicin siyasa da zai kawowa gwamnatinsa cikas.

Wannan na zuwa ne bayan Edison Ehie, kakakin majalisar dokokin jihar mai biyayya gare shi ya yi murabus.

Gwamna Fubara ya magantu kan rikicin Rivers
Gwamna Fubara na takun saka da Nyesom Wike Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Fubara ya ba da tabbacin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba game da jajircewarsa wajen samar da ingantaccen shugabanci.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya raba motoci 60 a jihar Kano, ya faɗi muhimmin dalili 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wadanda ke yaƙar gwamnatinsa suna son su dakushe mutanen Rivers ne da karfi da yaji, sannan su daƙile kawo cigaba, amma sun kasa.

Wane tabbaci Fubara ya ba mutanen Rivers?

Ya kuma ja hankalin al’ummar Rivers da kada su karaya kan rikicin da ke faruwa domin babu abin da zai hana shi tafiyar da al’amuran jihar cikin nasara.

Gwamna Fubara ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a cocin St Paul’s Archdeaconry Parish a garin Opobo a ranar jajibirin sabuwar shekara ta 2024 a ƙaramar hukumar Opobo/Nkoro (LGA), cewar PM News.

A kalamansa:

"Abin da suke so shi ne wannan jan biro, amma har yanzu yana tare da ni."
"Mu ne muka yi nasara saboda har yanzu muna sa hannu da jan biro.
"Muddin muna sanya hannu da jan biro, za a cigaba da samun cigaba a jihar Rivers.”

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Mazauna yankin Zamfara sun shafe shekaru 8 suna rikici a kan masalla, gwamna ya sa baki

Gwamna Fubara ya jaddada cewa, babu abin da zai hana gwamnatinsa isa ga inda ta dosa, domin an aza harsashin ginin da Allah ne kaɗai zai bayar da ikon kammala aikin ginin.

Rikicin Rivers: Fubara ya godewa Tinubu

Fubara ya nuna godiya ga shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa rawar da ya taka a lokacin da ya shiga tsakani domin taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a jihar Rivers.

A kalamansa:

"Kamar yadda na saba cewa, sai mutum mai dattako ne zai zama uba."
"Shi (Shugaba Tinubu) ya zama uba. A namu ɓangaren, za mu cigaba da ba shi dukkan goyon bayan da ya dace domin idan bai yi nasara a jihar Rivers ba, ba zai yi nasara a matsayinsa na shugaban ƙasa ba."

PDP Ta Gargaɗi Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta gargaɗi gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, kan rikicinsa da Nyesom Wike.

Jam'iyyar ta gargaɗi gwamnan kan aiwatar da yarjejeniyar da ya rattaɓa hannu domin kawo ƙarshen rikicinsa da tsohon gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng