Ikon Allah: Mazauna Yankin Zamfara Sun Shafe Shekaru 8 Suna Rikici a Kan Masalla, Gwamna Ya Sa Baki

Ikon Allah: Mazauna Yankin Zamfara Sun Shafe Shekaru 8 Suna Rikici a Kan Masalla, Gwamna Ya Sa Baki

  • Gwamnatin Zamfara ta yi rawar gani waje sake hada kan Musulmai a wani yankin da rikici ya raba tsakani
  • An sake bude masallacin juma’an da aka shekara 8 ba a yi amfani dashi ba saboda rikicin mazauna wani yanki
  • Rahoto ya bayyana irin kokarin da gwamnati ta yi na tabbatar da an kawo karshen duk wata husuma da ke tsakaninsu

Moriki, Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya warware rikicin shekara bakwai da ya kai ga rufe daya daga cikin manyan masallatan Juma’a na garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi.

Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa an rufe masallacin Juma’a sama da shekaru 7 da suka gabata sakamakon takaddamar da ta barke tsakanin bangarori biyu na jama’ar yankin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ya fitar ta ce gwamnan ya yi hakan ne domin magance matsalar rashin jituwa da ke tsakanin mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Bayan shafe shekaru 7 a kulle, an sake bude masallacin Juma'a da gwamnan PDP ya shiga lamarin

Gwamnan Zamfara ya warware rikicin masallacin Juma'a
Gwamna Lawal ya warware rikicin shekaru 8 | Hoto: @DDLDMForum
Asali: Twitter

Meye amfanin jituwa tsakanin jama’a?

Ya yi nuni da cewa gwamnan ya fahimci rawar da hadin kai da jituwa ke takawa wajen samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar:

“Gwamnatin jihar Zamfara ta ga ya dace ta shiga tsakani tare da daukar matakan warware duk wani abu da ke kawo rashin jituwa a tsakanin al’umma."

An yi sallar sake bude masallacin juma’a

Sheikh Abbas Moriki ne ya jagoranci sallar juma'a a sake bude masallacin, inda a hudubarsa ya yi tsokaci kan hadin kai tsakanin mutane, rahoton Leadership.

A nasa jawabin, Sarkin Moriki, Bashar Isma’ila Muhammad, ya mika godiyarsa ga Allah da ya shaida yadda aka sake bude masallacin yana raye.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar kan sa baki a kan lokaci wajen ganin an kawo karshen rikicin da ke tsakani.

Kara karanta wannan

"Muna daukar mataki": Gwamnatin Bayelsa ta yi martani kan auren yar shekara 4 da dan shekara 54

Ya zuwa yanzu dai ana sa ran hakan ya zama na karshe a duk wani rikicin da ke faruwa tsakanin mazauna yankin.

Rikicin Izala ya kai zuwa kotu

A wani labarin kuma, Jama'atul Izalatul Bid'ah wa Iqamatus Sunnah ta yi karin haske a game da abin da ya jawo rufe masallaci a Moriki.

A wani jawabi da kungiyar ta fitar a shafin Facebook a ranar Alhamis, an fahimci rigimar kungiyar ya yi dalilin daina salloli.

Kungiyar ta ce ba ta so yin magana a game da zancen ba domin an kai maganar kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel