Yadda Garaje da Gaggawa Suka Haifawa Tinubu Matsala a Farkon Mulkinsa Inji Jigon APC
- George Moghalu ya haska inda yake tunanin abin da ya zama matsala ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Babban ‘dan siyasar ce sabon shugaban kasar ya yi hanzari wajen kawo tsare-tsarensa da ya karbi mulki
- Cif Moghalu yana ganin kwalliya ba ta fara biyan kudin sabulu ba, shiyasa mutane su ke yawan kuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - George Moghalu ya taba zama babban mai binciken kudi a jam’iyyar APC, ya yi wata hira ta musamman da manema labarai.
A tattaunawar da ya yi da Daily Trust a watan nan, George Moghalu ya yi magana game da siyasa da mulkin Bola Ahmed Tinubu.
George Moghalu a kan mulkin APC da Tinubu
Cif George Moghalu ya nuna babbar matsalar da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya samu ita ce hanzari wajen nade-naden mukamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan siyasar ya gamsu cewa jama’a da yawa na kokawa da sabuwar gwamnatin Najeriya saboda tsadar rayuwa da ake ciki a yau.
Tsohon shugaban na hukumar NIWA ya ce garajen shugaba Bola Tinubu ya jawo hakan, duk da har yanzu gwamnatin ba ta dade ba.
Ra'ayin Moghalu a kan sabuwar gwamnatin APC
"Na yarda abubuwa ba su zo da sauki ba. Amma kuma duk da haka, zan ce gaggawan gwamnatin Tinubu ce matsalar.
Saboda gaggawar, mutane suna gani kamar gwamnatin ta shekara guda. Har yanzu watanni shida ne da ‘yan kai.
Ya yi saurin nada ministoci da wuf wajen daukar manyan matakai kan tallafin fetur da kudin kasar waje da harkar tsaro."
- George Moghalu
Moghalu ya ce ya kamata a jinjinawa Tinubu a kan haka, amma kuma ganin cewa ba a fara ganin tasirin tsare-tsaren ba, sai ake kuka.
APC a zaben gwamnan Anambra
A zantawarsa da jaridar, Moghalu ya nuna bai tsoron jam’iyyun adawa a zaben gwamnan jihar Anambra da za a gudanar a 2025.
Jagoran na APC ya ba jam’iyya mai mulki shawara cewa duk abin da za ayi, ta guji kakabawa al’umma ‘yan takaran da ba su kauna.
‘Dan takaran na zaben 2021 ya nuna karfa-karfa wajen bada tuta zai kashe APC a Anambra.
An kashe mutane a Najeriya
Majalisar Dinkin Duniya tayi kira ga hukumomin Najeriya su binciki kashe-kashen rayukan jama’an da aka yi a wasu kauyukan Filato.
Ana da labari Volker Turk ya nuna damuwarsa kan hare-haren ‘yan bindiga, ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta tashi tsaye a kasar.
Asali: Legit.ng