Shugaba Buhari ya nada sabon manajan darakta na NIWA

Shugaba Buhari ya nada sabon manajan darakta na NIWA

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wani jigon jam'iyyar APC, George Moghalu a matsayin sabon manajan darakta na hukumar NIWA

- Jagoran kula da hakokin hukumar Tayo Fadile, ya tabbatar da cigaban a Wani jawabi da ya saki a Lokoja a jiya Laraba

- Hakazalika Moghalu da tsohon manajan daraktan NIWA, Barista Danladi Ibrahim duk sun tabbatar da cigaban

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada babban mai binciken kudi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), George Moghalu a matsayin sabon manajan darakta na hukumar NIWA.

Babban manajan darakta na harkokin hukumar, Tayo Fadile, ya tabbatar da cigaban a Wani jawabi da ya saki a Lokoja a jiya Laraba, 2 ga watan Oktoba.

Fadile yace daga sabon manajan darakta, Moghalu har tsohon manajan daraktan NIWA, Barista Danladi Ibrahim duk sun tabbatar da cigaban.

KU KARANTA KUMA: Har gobe ni mai biyayya ne ga Buhari - Osinbajo

A wani labarin kuma Legit.ng ta ahoto a baya cewa Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya rantsar da sabbin masu bashi shawari na musamman 14 inda ya bukaci su mayar da hankali wurin magance matsalolin al'umma bisa son kai.

A yayin da ya ke jawabi a dakin taron 'yan fadarsa a ranar Laraba, Masari ya ce gwamnatin jam'iyyar APC ta al'umma ce saboda haka dole a mayar da hankali kan magance matsalolin talaka inda ya ce hakan ne yasa ya kirkiri sabbin ma'aikatu domin inganta aikin gwamnati a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng