Ministan Buhari, ‘Yan takara 11 sun ki yarda da sakamakon zaben da APC ta shirya a Anambra
- Mutum 11 da su ka shiga zaben fitar da gwani sun soki aikin da APC ta yi a Anambra
- George Moghalu ya yi magana a madadin masu neman takara, ya ce magudi aka tafka
- Sanata Chris Ngige ya soki zaben, ya ce mutane da yawa ba su iya kada kuri’arsu ba
Wasu 'ya ‘yan jam’iyyar APC da su ke neman tikitin shiga zaben gwamna a jihar Anambra, ba su amince da zaben fitar da gwanin da aka gudanar ba.
Jaridar Punch ta ce masu harin tutar jam’iyyar APC sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyya su shirya sabon zabe.
Mutum 11 daga cikin 14 da su ka shiga wannan takara sun ce ba su karbi sakamakon zaben da aka fitar ba, kuma suka ce za su kai korafinsu zuwa gaba.
KU KARANTA: Rikici ya biyo bayan zaben fitar da gwani da APC ta shirya a Anambra
Babu zaben da aka yi a APC
Shugaban hukumar NIWA, George Moghalu, ya na cikin wadanda suka shiga zaben tsaida ‘dan takarar, inda ya yi magana a madadin sauran mutane 11.
George Moghalu ya ce an yi magudi a wannan zabe da aka ce Sanata Andy Uba ya samu nasara.
Moghalu ya kira taron ‘yan jarida a garin Awka, ya ce babu zaben kirkin da aka gudanar domin a tsaida wanda zai rike wa APC tuta a babban zabe mai zuwa.
“Duk wanda ya ce an yi zaben fitar da gwani na gwamnan Anambra a karkashin APC, ba ya yi wa jam’iyya fatan alheri a zaben 6 ga watan Nuwamba.”
KU KARANTA: Sanatan Anambra, Uba ya sauya-sheka, ya koma APC
Ba zabe aka yi ba - Chris Ngige
Shi ma Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasa, Sanata Chris Ngige da yake hira da Channels TV a ranar Litinin, ya soki wannan zabe da aka shirya.
Chris Ngige ya ce shirin bogi kurum gwamna Dapo Abiodun da mutanensa su ka yi. Tsohon gwamnan ya ce ba a kawo kayan zabe bai sai karfe 6:30 na yamma.
“Ban iya zaben kowa ba, ban fito zabe ba domin ba a kawo kayan aiki ba. Ko lokacin da kayan zaben suka zo, na bogi aka kawo, ba ainihin takardun ba.”
Ngige yake cewa wadanda su ka shirya wannan aiki, suna kokarin jefa APC a rami a zaben bana.
A yau ne ku ka ji cewa jam'iyyar APC ta sake yin wani babban kamu a jihar Zamfara, inda ta dauke tsohon Sakataren jam’iyyar APGA na kasa, Dr. Sani Shinkafi.
Bayan shekaru kusan 20 ya na jam’iyyar hamayya, Sani Shinkafi ya dawo APC mai mulki. 'Dan siyasar ya ce gwamna Bello Matawalle ne ya karkato da ra'ayinsa.
Asali: Legit.ng