Majalisar UN Tayi Maganar Rayuka 190 da Aka Kashe a Najeriya, Tinubu Yana Hutu a Legas

Majalisar UN Tayi Maganar Rayuka 190 da Aka Kashe a Najeriya, Tinubu Yana Hutu a Legas

  • Kashe-kashen da ‘yan ta’adda su ka yi a karshen shekarar nan ya bar mutanen jihar Filato cikin jimami
  • Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta hana sake faruwar irin wannan ta’adi
  • Volker Turk ya fitar da jawabi na musamman cewa a gudanar da bincike na musamman, a dauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Plateau - Majalisar dinkin duniya ta yi tir da harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai a kauyukan jihar Filato a karshen shekarar nan.

Shugaban kula da hakkin bil adama a majalisar dinkin duniyan ya nuna hare-haren ya tada masa hankali, Daily Trust ta kawo rahoton.

Filato: Majalisar UN
Bola Tinubu a Majalisar dinkin duniya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mutane 195 sun mutu a kauyukan Filato

Ta’adin da aka yi tsakanin yammacin Asabar zuwa safiyar Talata ya yi sanadiyyar mutane kusan 200 a karamar hukumar Mangu a Filato.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Miyagu sun yi alkawarin sake kai hari bayan kashe mutum 195 a Filato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Volker Turk ya sanar da haka ne a wani jawabi da ya fitar a yammacin ranar Alhamis. Kafin nan Sarkin Musulmi ya soki hare-haren.

Mista Volker Turk ya nuna akwai matukar bukatar ayi gaggawar kawo karshen wannan kashe-kashe wanda ya ki ci kuma ya ki cinyewa.

Filato: Jawabin majalisar dinkin duniya

“Ina mai matukar damuwa da jeringiyar hare-haren ‘yan bindiga a kauyuka da-dama da ke jihar Filato."
"Ina kira ga hukumomin Najeriya su binciki wannan lamari da wuri kuma da kyau, bisa doron dokokin kare hakkin Bil Adama, kuma ayi adalci wajen hukunta wadanda aka samu da laifi a kotu."
"Dole a gaggauta kawo karshen wannan zalunci da yake yawon aukuwa. Sannan gwamnati ta dauki matakan kwarai wajen shawo kan asalin matsalolin tare da tabbatar da rikicin ba zai sake faruwa ba."

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya ta kama jami’inta kan mutuwar direban babban mota a Borno

- Volker Turk

Bola Tinubu ya tafi hutu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yana Legas domin hutun kirismeti a lokacin da abin ya faru, ya fitar da jawabi da ya samu labarin harin.

Baya ga Allah-wadai da ya yi, har yanzu Mai girma Bola Tinubu bai ziyarci kauyukan ba, amma Kashim Shettima ya samu zuwa a ranar Alhamis.

Za a sake kai hari a Filato?

Kuna da labari wani shugaba a kungiyar Middle-Belt Forum ya ce an jefa wasiku cewa za a kai wasu hare-haren a kauyukan da ke garin Mangu.

Stanley Kavwam ya ce jami’an tsaro sun san wadanda su ke da hannu wajen kashe Bayin Allah amma ana kama wadanda ba su yi laifin komai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng