Gwamna Abba, Kwankwaso da Mataimakin Shugaban Kasa, Shettima Sun Hadu a Kano
- Matimakin shugaban Najeriya ya kaddamar da wani gini da aka gyara a ofishin Gwamnan jihar Kano
- Kashim Shettima ya je Kano ne domin halartar jana’izar Rt. Hon. Ghali Umar Na'abba a makon nan
- Sanata Shettima ya hadu da tsohon gwamna kuma jigon NNPP watau Rabiu Kwankwaso a zuwansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Matimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kaddamar da ofishin Mai girma gwamna da aka sake gyarawa a jihar Kano.
Sanarwa ta fito daga shafin hadimin Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim cewa Kashim Shettima ya kaddamar da ginin ranar Laraba.
Abdullahi Ibrahim a jawabin da ya fitar a X, ya ce Kashim Shettima ya bude ginin tare da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi gyara a ofishin Gwamnan Kano
Sauran wadanda su ka taya shi su ne: Mai girma Sanata Barau Jibril, Sanata Kawu Sumaila da mataimakin gwamna, Aminu A. Gwarzo.
Ginin da aka sabunta yana kunshe da zauren majalisar zartarwa, dakin taro da katafaren daki na musamman da ke gidan gwamnati.
Hukumar dillacin labarai na kasa ta NAN ta ce Shettima ya yabawa gwamnan jihar Kano a kan yadda aka aiwatar da aikin da wuri.
Mataimakin shugaban kasar ya ce samar da gini na zamani irin wannan zai taimaka wajen jin dadin aikin ma’aikatan ofishin gwamnan.
“Ina taya Gwamna Yusuf da ‘yan majalisarsa murna a kan aikin da su ka yi da kyau.”
- Kashim Shettima
Kashim Shettima ya zo jana'iza
Salisu Hotoro, wani mai taimakawa Mai girma gwamnan da shawara ya ce Shettima ya zo garin Kano ne domin halartar jana’iza.
"Mai girma gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya karɓi bakuncin mataimakin shugaban kasa Alh. Kashim Shettima wanda ya zo Kano domin gaisuwar tsohon kakakin majalisar dokoki ta ƙara Hon. Ghali Umar Na'abba wanda Allah yayiwa rasuwa a daren jiya."
- Salisu Hotoro
Tarihin gyaran gidan gwamnati
Wani rahoto da aka fitar ya nuna a shekarar 1967 aka fara gina ofishin a sa’ilin da Abdu Bako yake gwamnan jihar Kano a mulkin soja.
Mai girma Abdullahi Ganduje ya yi wasu gyare-gyare a ofishin mataimakin gwamnan Kano da ya karbi mulki a shekarar 2015.
Bidiyon Kwankwaso da Kashim Shettima
Legit ta ga bidiyo cewa Rabiu Musa Kwankwaso PhD FNSE ya hadu da Shettima da sauran musulmai a wajen jana’izar Ghali Na' Abba.
Sauran wadanda su ka halarci jana’izar sun hada da tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.
Kano tayi rashin Ghali Na'abba
Rahotanni sun zo a baya cewa Rt. Hon. Ghali Umar Na'abba ya rasu a safiyar Laraba kuma an birne shi tun a jiya a mahaifarsa ta Kano.
Rt. Hon. Ghali Umar Na'abba ya rasu a birni Abuja ne yana shekara 65 da haihuwa.
Asali: Legit.ng