Kaddara Ta Riga Fata: Jerin 'Yan Takara 9 Sa Suka Mutu Daf Da Shirye-Shiryen Zabe a 2023
- Wasu daga cikin masu neman tsayawa takarar siyasa a zabuka dabam-dabam a shekarar nan ta 2023 sun rasu
- ‘Yan siyasan sun mutu ne kafin shiga babban zabe, bayan sun samu takara a karkashin jam’iyyun da su ke ciki
- A dalilin haka dole jam’iyyun su ka canza wadanda aka ba tikiti, shakka babu mace-macen nan sun taba jama’a
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
1. ‘Dan takaran Gwamna a Abia
Ana saura wata guda a shiga zaben gwamnoni sai Farfesa Uche Ikonne ya rasu. Kafin rasuwarsa shi ne zai yi wa PDP takara a jihar Abia a 2023.
Watakila hakan ya taimaka wajen nasarar da Alex Otti da jam’iyyar LP ta samu a Abia.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. ‘Dan takaran Sanata a Enugu
A watan Fabrairun 2023 ne Oyibo Chukwu ya rasu a wani hari da aka kai masa a cikin mota. Maharan sun kashe Chukwu tare da direbansa.
Mutuwar ‘dan takaran na jam’iyyar LP ya sa INEC ta dakatar da zaben Sanata a Enugu.
3. ‘Dan takaran gwamna a Adamawa
Alhaji Aliyu Maina ne wanda jam’iyyar NRM ta tsaida ya yi mata takarar gwamnan jihar Adamawa a zaben 2023, kafin lokacin rai ya yi halinsa.
Sakataren yada labaran NRM na kasa, Olusola Afuye ya tabbatar da rasuwar Aliyu Maina.
4. ‘Dan takaran majalisa a Kano
Kwanaki kadan su ka rage ayi zabe sai Kamilu Ado Isa ya rasu. Marigayin ya bar duniya zai yi wa NNPP da Wudil-Garko takarar ‘dan majalisa.
A dalilin rasuwar tsohon jami’in tsaron aka dauko yaronsa wanda shi ya lashe zaben.
Sauran ‘yan takaran da su ka rasu a 2023:
5. Barrister Abba Bello Haliru
6. Mathew Akawu
7. Pharm. Ejikeme Omeje
8. Christopher Elehu
9. Arthur Egwim
Menene abin da doka ta ce?
Sashe na 34 na dokar zaben 2022 ya ce idan ‘dan takara ya mutu kafin a fara zabe, INEC za ta dakata na kwana 14 jam’iyya ta canza ‘dan takara
Idan kuwa bayan an shiga zabe ne sai ‘dan takara ya mutu, za a dauko abokin gaminsa.
Tasirin kotu wajen samun mulki
Ana da labarin yadda Emeka Ihedioha yana mulki aka tsige shi, sannan ana gobe David Lyon zai zama gwamna aka soke zaben shi a Bayelsa.
Rotimi C. Amaechi ya zama Gwamnan Ribas ne saboda kotun koli ta tsige wanda aka zaba a 2007. Irin hakan ta faru da Bello Matawalle a Zamfara.
Asali: Legit.ng