Kanin Ministan Tinubu Ya Yunkuro Don Gadar Kujerar Yayansa Ta Sanata, Ya Fadi Dalili
- Austin Umahi, kani ga Ministan ayyuka, Dave Umahi ya nuna sha’awar tsayawa takara don gadar kujerar yayanshi
- Umahi ya nuna sha’awar neman kujerar ce bayan Sanata Umahi ya bar kujerar don karbar mukamin Minista
- Austin ya bayyana kudirinsa ne a yau Litinin 25 ga watan Disamba yayin ganawa da manema labarai a Abakaliki da ke jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ebonyi – Kanin tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya shirya gadar kujerar Sanata ta yayansa a jihar.
Cif Austin Umahi ya nuna sha’awar neman kujerar ce bayan Sanata Umahi ya bar kujerar don karbar mukamin Minista, cewar Punch.
Mene Umahi ya ke cewa kan neman kujerar?
Kafin zama Minista, Umahi ya wakilci mazabar Ebonyi ta Kudu wanda a yanzu hukumar INEC ta shirya gudanar da zabe a watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Austin ya bayyana kudirinsa ne a yau Litinin 25 ga watan Disamba yayin ganawa da manema labarai a Abakaliki da ke jihar.
Umahi ya ce ya tabbatar da cewa ya dace da kujerar kuma ya na da dukkan abin da ake nema don dare wa kan kujerar, cewar Independent.
Ya ce:
“Bin tsarin dimukradiyya shi ne kadai hanyar samar da sanatan da zai wakilci mazabar a nan gaba.
“Zan ba da dukkan gudunmawa wurin mulkar mutane ganin yadda na kware a harkar siyasa da kuma kasuwanci.”
Austin ya rike Darakta Janar na jam’iyyar APC a babban zaben da aka gudanar a 2023 inda ya ce shi ya fi dace wa da kujerar, cewar Tribune.
Halin kunci: Ubangiji ba zai yafe maka ba, Fitaccen malamin addini ya taba Tinubu kan salon mulkinsa
Mene dalilin tsayawa takarar Umahi?
Ya kara da cewa:
“Muna tsarin dimukradiyya ce, kuma ina son dukkan magoya baya na da su yi min addu’a don samun nasara a zabe.
“Na fito daga karamar hukumar Ohaozara inda a nan ne jam’iyyar ta tura kujerar sanatan da za a yi zabe.”
Umahi ya ce zai tsaya takarar ce don ci gaban jihar ba wai don karan kansa ba inda ya ce wannan ne lokacin da ya dace da a kawo gyara.
Lalong ya karbi rantsuwa a matsayin Minista
A wani labarin, Tsohon gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya karbi ratsauwa a matsayin Sanata daga jihar.
Lalong ya ajiye mukamin Ministan Kwadago don karbar kujerar Sanata bayan ya yi nasara a kotu.
Asali: Legit.ng