Halin Kunci: Ubangiji Ba Zai Yafe Maka Ba, Fitaccen Malamin Addini Ya Taba Tinubu Kan Salon Mulkinsa

Halin Kunci: Ubangiji Ba Zai Yafe Maka Ba, Fitaccen Malamin Addini Ya Taba Tinubu Kan Salon Mulkinsa

  • Shahararren Fasto a Najeriya ya gargadi Shugaba Tinubu kan salon mulkin da ya ke yi a kasar
  • Fasto Mathew Hassan Kukah ya ce Ubangiji ba zai yafe wa Tinubu ba idan har bai kawo sauyi a yanayin yadda ake a kasar ba
  • Faston ya bayyana haka ne yayin jawabin bikin Kirsimeti a yau Litinin 25 ga watan Disamba a Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Fitaccen Fasto a Najeriya, Mathew Hassan Kukah ya gargadi Shugaba Tinubu kan irin mulkin da ya ke yi a kasar.

Kukah ya ce Ubangiji da sauran 'yan Najeriya ba za su yafe wa shugaban ba idan har bai kawo sauyi a kasar ba.

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun kai farmaki wurin ibada, sun halaka bayin Allah da dama a Ebonyi

Kukah ya gargadi Tinubu kan salon mulkin d ya ke yi a Najeriya
Kukah ya tura sakon gargadi ga Shugaba Tinubu. Hoto: Bola Tinubu, Mathew Hassan Kukah.
Asali: Facebook

Mene Kukah ke cewa kan Tinubu?

Faston ya bayyana haka ne yayin jawabin bikin Kirsimeti a yau Litinin 25 ga watan Disamba a Sokoto, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci Tinubu ya yi amfani da baiwarsa wurin tabbatar da kawo karshen matsalar bambance-bambancen addini da kabilanci.

Ya ce:

"Kai ne direba a yanzu da kake jan motar Najeriya, ya kamata ka kawo karshen matsalar bambance-bambancen addini da kabilanci.
"Ka samu isasshen lokacin da zaka amsa dukkan kiraye-kirayen mutane, kaddarar Najeriya a yanzu ta na hannunka.
"A yanzu ba ka da wani uzuri, ubangji da tarihi ko mutanen Najeriya ba za su yafe maka ba idan ba ka yi abin da ya dace ba."

Mene Kukah ya ce kan tallafi?

Kukah ya ce 'yan Najeriya yanzu sun cire tsammanin cewa gwamnati zata cire son rai don ta yaki cin hanci da rashawa, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Akwai haske a 2024: Tinubu ya yi gagarumin alkawari gabannin shiga sabuwar shekara, ya fadi dalili

Har ila yau, Kukah ya ce maganar ba da tallafi babu abin zai rage a wahalakun da ake ciki sai dai idan gwamnati ta shirya kawo gyara wanda ya turnuke shugabanci.

Tinubu ya yi alkawari ga 'yan Najeriya

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa akwai haske a tattare da sabuwar shekarar da za a shiga ta 2024.

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin tabbatar da ci gaba da ba da tallafi don rage wa jama'a radadin da suke ciki.

Shugaban ya bayyana haka ne a yau Litinin 25 ga watan Disamba yayin jawabin bikin Kirsimeti a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel