‘Yan Siyasan PDP da APC da Su ka Halarci Zaman Sulhun da Tinubu Ya yi wa Wike da Fubara
- Bola Ahmed Tinubu ya sake yin zama da kusoshin siyasar Ribas domin a birne sabanin da ya jawo rikici a jihar
- Siminalayi Fubara da Nyesom Wike sun yi zaman sulhu tare da jagororin jam’iyyun PDP da APC a Aso Villa
- Sauran jami’an gwamnati da shugaban majalisar Ribas sun samu halartar zaman da aka yi domin a dinke baraka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
FCT, Abuja – A makon nan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya wani taron manyan masu ruwa da tsaki a siyasar Ribas.
A rahoton, Legit ta bibiyi duka wadanda aka yi wannan zama da su a fadar Aso Rock Villa har aka iya cin ma wasu yarjejeniya takwas.
1. Bola Tinubu
Da farko dai shugaban kasa ne ya kira taron a matsayinsa na uban kowa, duk da wasu suna ganin cewa bai da hurumin tsoma baki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Kashim Shettima
Mataimakin shugaban Najeriya yana zaune aka yi zama domin sasanta Ministan Abuja da gwamnan Ribas, amma da alama bai cikin masu sa hannu.
3. Femi Gbajabiamila
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya halarci taron, sai dai shi ma babu sa hannunsa a takardar yarjejeniyar sulhun.
4. Nuhu Ribadu
Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu yana fadar Aso Villa aka yi zaman, kuma an ga sa hannunsa a takardar zaman.
5. Sim Fubara
Gwamnan jihar Ribas, Simi Fubara ya yarda da yarjejeniya takwas da aka dauka kamar yadda sa hannunsa a farkon takardar ya tabbatar mana.
6. Nyesom Wike
Ministan harkokin birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya isa wajen taron da kimanin karfe 7:00. Shi ne dama ya samu sabani da Simi Fubara.
7. Ngozi Odu
Mataimakiyar gwamnar Ribas, Farfesa Ngozi Odu wanda ba a san matsayarta ba, ta na wajen zaman kuma ta na cikin wadanda su ka sa hannu.
8. Martin Chike
An ga sa hannun shugaban majalisar dokokin jihar Ribas, Rt. Hon. Martin Chike wanda hakan ya tabbatar da cewa yana wajen zaman sulhun.
9. Tony Okocha
A matsayinsa na shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya a jihar Ribas, Tony Okocha ya je taron sulhun da ya hada ‘ya ‘yan PDP da na APC.
10. Aaron Chukwuemeka
Shi ma shugaban PDP mai mulki a Ribas na riko, Aaron Chukwuemeka ya rattaba hannu a yarjejeniyar duk da jam’iyyarsa ta soki matsayar taron.
Simi Fubara v Nyesom Wike
A taron da aka yi a Aso Villa, an samu labari Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Simi Fubara kaca-kaca saboda ya rusa ginin majalisar dokoki.
Bayan an cin ma yarjejeniya, Gwamna Simi Fubara ya saduda da sunan cewa zaman lafiya ake nema a Ribas, hakan bai yi wa PDP dadi ba.
Asali: Legit.ng