Musulmai Sun Yi Addu’ar Samun Nasarar Gwamna Kirista Yayin da Ake Shirin Yanke Hukunci, an Yi Bayani

Musulmai Sun Yi Addu’ar Samun Nasarar Gwamna Kirista Yayin da Ake Shirin Yanke Hukunci, an Yi Bayani

  • Daruruwan Musulmi ne su ka fito a jihar Plateau don nuna goyon baya ga Gwamna Caleb Mutfwang
  • Musulman sun yi addu’ar ce don samun nasarar gwamnan a Kotun Kli da ake dakon shari’ar nan gaba
  • Hausa Legit ta ji ta bakin wani jigon PDP da ke garin Jos wanda ya na daga cikin wadanda suka yi addu'o'in

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau – Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a jihar Palteau, Al’ummar Musulmi sun yi addu’ar samun nasara ga Gwamna Caleb Mutfwang.

Al’ummar Musulmin da su ka yi addu’ar sun fito daga dukkan kananan hukumomi 17 da ke jihar.

Al'ummar Musulmi sun yi addu'ar samun nasara ga Gwamna Caleb a Plateau
Musulmai sun yi addu'a na musamman a Plateau ga Gwamna Caleb. Hoto: Caleb Mutfwang, Sani Abubakar.
Asali: Facebook

Mene dalilin addu'ar a Jos?

Kara karanta wannan

Ana saura awanni kadan a yanke hukunci, PDP a jihar Arewa ta mika lamarinta ga Allah, ta yi gargadi

Addu’ar ta musamman an gudanar da ita ne a yau Laraba 20 ga watan Disamba don samun nasarar gwamnan, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke magana kan addu’ar da aka gudanar a babban masallacin Juma’a a Jos, tsohon mamban Majalisar jihar, Sani Abubakar ya bayyana dalilin yin addu’ar.

Sani ya ce sun yi adduar ce don kara wa gwamnan kwarin gwiwar ci gaba da ayyukan alkairi a jihar, cewar Daily Post.

Ya ce gwamnan ya dauko hanyar kawo sauyi a jihar ganin yadda ya ke ayyukan ci gaba a jihar da ke da tasiri kan al’ummar jihar.

Meye martanin Musulman a Jos?

Ya ce:

“A matsayinmu na Musulmai, mun yadda da alfarmar Alkur’ani kuma muna koma wa gare shi lokacin da muke cikin wani hali.
“Mun taru a nan don karanta wasu ayoyi a cikin Alkur’ani don neman taimakon Allah da ci gaban wannan gwamnati.

Kara karanta wannan

Bayan na Kano, Kotun Koli ta sake sanya ranar raba gardama a shari'ar neman tsige gwamnan Arewa

“Wannan taro ya na nuna cewa Musulmai a jihar Plateau su na kaunar gwamnansu da kuma nuna goyon baya ga ci gaban gwamnatin.”

Legit Hausa ta ji ta bakin wani jigon PDP, Jibrin Madaki kan wannan lamari:

Madaki ya ce shi Musulmi ne kuma ya na daga cikin wadanda suka yi taron addu'ar neman nasara ga Caleb Mutfwang.

Yace wannan gwamnati ta na kawo ci gaban jihar ba tare da bambanci ba a tsakanin 'yan jihar.

Ya ce:

"Ni ina daga cikin wadanda suka yi addu'ar kuma ina goyon bayan haka saboda nasarar wannan gwamnati.
"Wannan tafiya ce ta 'Plateau Project' wanda ita ta kawo Lalong da kuma Mutfwang wanda ya na tafiya da kowa a Plateau babu bambanci."

Ya kara da cewa Gwamna Caleb ya yi zama da al'ummar Musulmai wanda kowa ya sani ba shi da wani bambanci a zuciyarsa.

Caleb ya yi martani kan ganawarshi da Tinubu

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar karshe ta neman tsige gwamnan PDP, ta ba da bahasi

A wani labarin, Gwamna Caleb Mutfwang ya yi martani kan zargin cewa ya gana da Shugaba Tinubu kan hukuncin Kotun Koli.

Wannan na zuwa ne bayan an yada cewa gwamnan ya gana da Tinubu don samun nasara a kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.