Bayan Shekaru 14 da Kiran Yar'adua Ya Yi Murabus, Gwamnan APC Ya Gamu da Irin Jarrabawar Marigayin

Bayan Shekaru 14 da Kiran Yar'adua Ya Yi Murabus, Gwamnan APC Ya Gamu da Irin Jarrabawar Marigayin

  • Marigayi Tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'adua ya sha suka lokacin da ya ke jinya a kasar Saudiyya
  • Daga cikin masu ihun sai ya yi murabus akwai Gwamna Rotimi Akeredolu a 2009 lokacin ya na shugaban kungiyar NBA
  • Bayan shekaru 14, Akeredolu ya gamu da jarrabawa irinta marigayin inda shi ma yanzu ake kiraye-kirayen ya yi murabus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Gwamna Rotimi Akeredolu a shekarar 2009 ya yi ta kiraye-kirayen cewa sai marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa 'Yar'adua ya yi murabus.

Akeredolu wanda a lokacin shi ne shugaban Kungiyar Lauyoyi a Najeriya (NBA) ya yi kiran ne saboda rashin lafiyar Yar'adua.

Kara karanta wannan

Tsohon Ministan Buhari ya ci gyaran Shugaba Tinubu a kan abubuwa 2 da ya aikata a ofis

Akeredolu ya gamu da jarabawa bayan caccakar marigayi Yar'adua a 2009 ya yi murabus
Gwamna Akeredolu na ci gaba da jinya a kasar Jamus. Hoto: UMaru Yar'adua, Rotimi Akeredolu.
Asali: Facebook

Mene Akeredolu ke cewa kan Yar'adua?

Hakan ya faru ne bayan tsohon shugaban ya shafe watanni a Saudiyya don neman lafiya, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin wani taro a shekarar, Akeredolu ya ce Najeriya ta doshi hanyar durkushewa inda ya bukaci marigayin ya yi murabus.

Ya ce duk son mulkar Najeriya da ke son yi ba zai yi da rashin lafiya ba, inda ya ce suna addu'ar samun saukin shugaban ya dawo gida ya kuma yi murabus.

Mene yanzu ke damun Akeredolu?

Sai gashi yanzu bayan shekaru 14, Akeredolu ya gamu da jarrabawa irinta tsohon shugaban kasar wanda shi ma yanzu ya ki yin murabus daga kujerarshi.

Akeredolu ba ya iya gudanar da harkokin mulki tun watan Yunin wannan shekara bayan ya mika mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Tun farko ya nemi tafiya kasar Jamus na kwanaki 21 don neman lafiya amma daga baya ya kara zamansa don ci gaba da karbar kulawa.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

Gwamnan ya sake dawo wa a watan Satumba inda ya ci gaba da zama a jihar Oyo madadin Ondo, Abatimedia ta tattaro.

Daga bisani a watan Disamba ya sake fita kasar Jamus bayan mika mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Tinubu ya sake shiga rikicin siyasar Ondo

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake tsoma baki a rikicin siyasar jihar Ondo.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ke saka baki don kawo karshen rikicin da ya addabi jihar.

A baya, Tinubu ya yi zama da wadanda abin ya shafa amma daga bisani rikicin ya kara kamari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.