Gwamnan Arewa Ya Gana da Tinubu da Shugaban Alkalai Kan Hukuncin Kotun Koli? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnan Arewa Ya Gana da Tinubu da Shugaban Alkalai Kan Hukuncin Kotun Koli? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamna Caleb Mutfwang na Plateau ya yi martani kan zargin cewa ya gana da Shugaba Tinubu yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli
  • Har ila yau, an yi ta yadawa cewa gwamnan ya gana da shugaban alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola inda ya karyata hakan
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Musa Ashoms ya fitar a yau Talata 19 ga watan Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau – Gwamnatin jihar Plateau ta karyata jita-jitar cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya gana da Tinubu kan hukuncin Kotun Koli.

Martanin na zuwa ne bayan an yada cewa gwamnan ya gana da Tinubu da kuma shugaban alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola.

Kara karanta wannan

Bikin Kirsimeti: Gwamnan APC ya ba ma'aikata hutun kwanaki 14

Gwamna Caleb ya yi martani kan ganawarshi da Tinubu saboda Kotun Koli
Gwamna Caleb ya magantu kan jita-jitar ganawa da Tinubu. Hoto: Caleb Mutfwang, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene Gwamna Caleb ya ce kan ganawa da Tinubu?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Musa Ashoms ya fitar a yau Talata 19 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ashoms ya ce wannan labari ba shi da tushe bare makama inda ya kara da cewa bayan yada cewa PDP ba ta da tsari a jihar, cewar Tribune.

Masu yada jita-jitar ba su gajiya ba inda su ka sake samun wata hanya ta ruguza siyasar jihar.

Musa har ila yau, ya musanta cewa Gwamna Caleb ya yi alfaharin nasara a kujerarshi bayan ganawar da Shugaba Tinubu, cewar Punch.

Wane tabbaci ya bayar kan Gwamna Caleb?

Ya ce yadda APC ke karairayi musamman ta fannin da ya shafi PDP a Plateau ya nuna yadda ta matsu ta kwace mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya soki gwamnan PDP a zaman sulhu da mai gidansa, ya kawo misalin rikicin siyasarsa a legas

Ya ce:

“Babu kokwanto Gwamna Caleb Mutfwang ya na samun goyon baya daga ‘yan jihar saboda irin ayyukan alkairi da ya ke yi.
“Ba abin mamaki ba ne a gano ‘yan adawa su rikice don ganin sun yi aiki tare da shi a inuwa daya.”

Ashoms ya ce Gwamna Caleb ya samu nasara ce a ranar 18 ga watan Maris wanda jama’ar gari su ka zabe shi.

APC ta yi martani kan zargin ganawarta da NNPP

A wani labarin, Jam’iyyar APC mai mulki ta yi martani kan zargin ta gana da NNPP kan shari’ar zaben jihar Kano.

An yada cewa jam’iyyun sun yi ganawar ce don yarjejeniyar Abba Kabir ya koma APC don a bar masa kujerarshi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.