‘Yan Takaran APC a 2023 Sun Kama Shirye Shiryen Tazarcen Bola Tinubu a Zaben 2027

‘Yan Takaran APC a 2023 Sun Kama Shirye Shiryen Tazarcen Bola Tinubu a Zaben 2027

  • A yau ne za a kaddamar da kungiyar 2023 APC Presidential Aspirants domin shirin zaben shugaban kasa a 2027
  • Wasu da su ka yi takara da Bola Tinubu a zaben da ya gabata sun ce za su goyi bayan shi domin ya zarce cikin sauki
  • ‘Yan siyasan za su zauna da mutanen Najeriya da ke kasar waje domin a fara shirin yadda APC za ta iya lashe zabe

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Wasu ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a jam’iyyar APC sun nuna za su goyi bayan Bola Ahmed Tinubu ya zarce.

A ranar Litinin, Leadership ta rahoto ‘yan siyasar suna cewa za su hakura da burinsu domin Bola Ahmed Tinubu ya samu tazarce.

Kara karanta wannan

Kano: An yi yarjejeniya da Abba Kabir don bar masa kujerarshi saboda ya koma APC? Gaskiya ta fito

Bola Tinubu a Zaben 2027
Yakin zaben Bola Tinubu Hoto: OfficialAPCNigeria
Asali: Facebook

Kaddamar 2023 APC Presidential Aspirants

Wadannan masu neman mulki a jam’iyyar APC sun kafa kungiya da su ka kira 2023 APC Presidential Aspirants da za a kaddamar a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yau, 18 ga watan Disamba 2023, za a bude kungiyar a Transcorp Hilton a garin Abuja yayin da wasu su ka fara buga gangar 2027.

Su wanene ke goyon bayan Tinubu?

Shugaban wannan tafiya shi ne tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yerima kuma wanda ya nemi tikiti a APC a zaben 2023.

Rahoton ya ce a tafiyar akwai Dr. Nicholas Felix wanda ya yi takara da Bola Tinubu a bana, shi ne ‘yan autan cikin masu neman tuta.

‘2023 APC Presidential Aspirants’ ta ce za ta fara wannan shiri ne saboda sun hakura da burinsu, sun yi na’am da tafiyar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya da Gandujiyya da sauran rigingimun siyasar da suka fi dadewa a Najeriya

Tinubu zai samu tazarce a saukake

‘Yan siyasar sun ce ‘yan kungiyarsu sun hakura za su fasa neman mulki a zaben 2027 domin shugaban kasa ya zarce cikin sauki.

A jawabin da kungiyar ta fito, tayi alkawarin taimakawa Mai girma Bola Tinubu a zabe mai zuwa da ake sa ran zai nemi ya zarce.

Shirin ‘2023 APC Presidential Aspirants’

Vanguard ta ce za kuma ayi amfani da damar bude kungiyar wajen shirya liyafar karshen shekara domin a goyi bayan gwamnati.

Kungiyar nan za tayi uwa da makarbiya wajen ganin an yada manufofin gwamnati mai-ci tare da hada-kai da 'yan Najeriya da ke ketare.

Gwamnoni da kotun koli

Kun ji labari Emeka Ihedioha yana mulki aka tsige shi, sannan ana gobe David Lyon zai zama gwamna aka soke zaben shi a jihar Bayelsa.

Dole aka rantsar da Bello Matawalle a Zamfara saboda APC ba ta shirya zaben gwani a 2019 ba, irin abin da ke neman faruwa da Filato a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng