2023: Bayan Fasto Bakare, Wani Malamin Addini Ɗan Shekara 40 Ya Sake Siyan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a APC

2023: Bayan Fasto Bakare, Wani Malamin Addini Ɗan Shekara 40 Ya Sake Siyan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a APC

  • Mr Nicholas Felix, matashin fasto kuma dan kasuwa mazaunin Amurka ya shiga jerin yan takarar shugaban kasa a APC
  • Felix, ya lale kudi Naira miliyan 65 ya siya fom din takarar shugaban kasa inda ya samu ragwame kasancewarsa matashi a jam'iyyar ta APC
  • Bayan siyan fom dinsa, ya yi alkawarin zai tattaro kwararru a gida da waje don magance matsalolin Najeriya idan an zabe shi shugaban kasa

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Nicholas Felix, ya yi alkawarin magance matsalar tsaro a Najeriya idan an zabe shi a 2020, Premium Times ta rahoto.

Mr Felix, wanda ya furta hakan a Abuja bayan siyan fom din takararsa na shugaban kasa a 2023, ya ce samar da tsaro a kasar zai warware wasu matsalolin da dama har da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Dan Marigayi Abiola Ya Shiga Jerin Masu Son Gaje Kujerar Buhari, Ya Siya Fom Din Takara

2023: Bayan Fasto Bakare, Wani Malamin Addini Ɗan Shekara 40 Ya Sake Siyan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a APC
2023: Malamin Addini Ɗan Shekara 40 Ya Sake Siyan Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a APC. Hoto: Pulse Ng
Asali: Twitter

Ina son zama shugaban kasa ne domin in kawo canji a Najeriya - Felix

Dan takarar shugaban kasar, mazaunin Amurka kuma mai Cocin Miracle Center International Inc. ya ce burinsa shine ya zama shugaban Najeriya ya kawo canji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Felix yana da hedkwatar cocinsa a New York, a Amurka da rassa a New Jersey, Texas, Atlanta da kuma Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta rahoto cewa dan takarar shugaban kasar ya biya Naira miliyan 65 na fom din takarar.

Ya mika godiyarsa ga Shugaba Muhammadu Buhari saboda yi wa matasa rangwamen kashi 50 cikin 100 na kudin fom din don matasan APC.

"Na yanke shawarar yin takarar shugaban kasar Najeriya ne don in kawo canji da taimakon dokar rage shekarun yin takara.
"Kuma, domin tara kwararru daga gida da kasashen waje domin su bada gudunmawa don cigaban kasarmu," in ji shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Ba wannan karon bane takararsa na farko

Mr Felix, wanda dan takarar shugaban kasa ne a zaben 2019 karkashin jam'iyyar PCP bayan Muhammadu Buhari na APC da Abubakar Atiku na PDP, ya samu kuri'u 110,196.

Ya ce yana kyautata zaton APC za ta bashi damar cika burinsa na zama shugaban kasa ya kuma kawo canjin da yan kasar ke so.

Ya yi alkawarin magance matsalar lantarki, rashin tsaro da wasu kallubale da ke adabar kasar.

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Kara karanta wannan

Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Ya Yi Rajista Da APC a Mazabansa, Majiya

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164