Gwamnan Arewa Ya Zargi Jam’iyyar Adawa a Jiharsa da Neman Ta da Zaune Tsaye Kan Hukuncin Kotun Zabe
- Gwamnatin jihar Nasarawa ta zargi jam’iyyar adawa ta PDP da neman jawo tashin hankali kan hukuncin Kotun Daukaka Kara a jihar
- Gwamna Sule ya ce PDP na neman amfani da bambance-bambancen addinai da kabilanci a jihar don kawo rudani a jihar
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan, Mista Peter Ahemba ya fitar a jiya Juma’a 15 ga watan Disamba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Nasarawa – Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya zargi jam’iyyar PDP da kokarin ta da zaune tsaye kan hukuncin kotu.
Gwamnan ya ce PDP na neman amfani da bambance-bambancen addinai da kabilanci a jihar don kawo rudani.
Mene dalilin zargin PDP a jihar?
Wannan na zuwa ne yayin da Kotun Daukaka Kara ta yanke hukunci inda ta tabbatar da nasarar Gwamna Sule na jam’iyyar APC a kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan, Mista Peter Ahemba ya fitar a jiya Juma’a 15 ga watan Disamba, cewar Leadership.
Ahemba ya ce jam’iyar PDP na kokarin bata sunan bangaren shari’a ta ko wane hali da kuma gudanar da zanga-zanga a Lafia.
Wane zargi aka yi kan PDP?
Ya ce hakan ya tabbata bayan sun dauki nauyin wasu masu zanga-zanga da sunan gammayyar ‘yan asalin jihar Nasarawa.
Peter ya ce PDP na ci gaba da bin ko wace hanya don ganin ta cimma burinta tun farkon kamfen zaben watan Maris da aka gudanar.
A karshe, ya yi Allah wadai da neman mulki da PDP ke yi ta ko wane hali inda ya bukaci jami'an tsaro su shiga ciki, cewar Daily Post.
‘Yan PDP sun yi addu’ar neman sa’a
A wani labarin, gamayyar Musulmai da Kirista sun fito tattaki da kuma fara azumin neman nasara gabannin hukuncin Kotun Daukaka Kara.
Masu addu’ar sun bayyana cewa akwai wadansu da suka shirya kwace nasarar David Ombugadu na jam’iyyar PDP a jihar.
Hakan ya biyo bayan yanke hukunci da Kotun ta yi inda ta bai wa dan takarar PDP nasara a kotun da kuma rusa zaben Gwamna Sule na jam’iyyar APC.
Asali: Legit.ng