Gwamnan APC Ya Tabbatar da Barin Ciyamomi 21 da Kansiloli 239 Ofisoshinsu, Ya Fadi Dalili
- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya tabbatar da murabus din ciyamomin kananan hukumomi 21 a jihar
- Akalla ciyamomin 21 ne su ka ajiye mulki yayin da kansiloli 239 su ma su ka bar ofisoshinsu
- Wannan na zuwa ne yayin da wa'adinsu na shekaru uku ya kare kuma shi ma gwamnan ke shirin barin kujerar mulki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya tabbatar da cewa ciyamomi da kansiloli a jihar sun ajiye mukamansu.
Gwamnan ya ce ciyamomi 21 da kansiloli 239 ne su ka bar ofisoshinsu a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba.
Yaushe su ka kama aiki a Kogi?
Wannan na zuwa ne yayin da wa'adin shekaru ukunsu ta cika a jihar tun bayan hawan gwamnan karo na biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan kananan hukumomi a jihar, Barista Ozigi Deedat shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a birnin Lokoja.
Ciyamomin da kansilolin sun sha rantsuwa ne tun a ranar 15 ga watan Disambar 2020, cewar Tribune.
Deedat ya taya ciyamomin murna yayin da su ka kammala wa'adinsu cikin nasara inda ya musu fatan alkairi.
Sai dai Deedat bai yi martani kan yaushe za a sake zaben kananan hukumomi ba yayin da gwamnatin Yahaya Bello ke shirin tattare kayansu a gidan gwamnati.
Wane martani gwamnatin jihar ta yi?
Ya ce:
"A madadin ma'aikatar kananan hukumomi da masarautun gargajiya mu na taya ciyamomi 21 da su ka kammala wa'adinsu cikin nasara.
"Tabbas kun ba da naku gudunmawa a wannan jihar wurin samar da abubuwan more rayuwa da dan kudaden da mu ka samu.
"Na taya ku murna kuma ina muku fatan alkairi a nan gaba."
Sai dai abin da ba a sani ba shi ne ko Gwamna Yahaya Bello zai kafa kwamitin rikon kwarya a kananan hukumomin ko sabanin haka, cewar The Source.
Bello ya sake kirkirar sabuwar ma'aikata
A wani labarin, Saura makwanni kadan ta bar kujerar mulki, Yahaya Bello ya sake kirkirar sabuwar ma'aikata.
Bello ya kirkiri ma'aikatar jin kai da walwala don rage radadin talauci da ta addabi jihar baki daya.
Asali: Legit.ng