Rikicin Wike da Fubara Ya Dauki Sabon Salo Yayin da Atoni Janar na Ribas Ya Yi Murabus

Rikicin Wike da Fubara Ya Dauki Sabon Salo Yayin da Atoni Janar na Ribas Ya Yi Murabus

  • Atoni janar na jihar Ribas kuma kwamishinan shari'a, Zacchaeus Adangor, ya yi murabus daga mukaminsa
  • Adangor ya aika takardar murabus dinsa mai kwanan wata 14 ga watan Disamba, 2023 zuwa ga Gwamna Siminalayi Fubara
  • Adangor ya ce ya yi murabus daga kujerarsa ne saboda wani dalili nasa na kashin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Port Harcourt, jihar Rivers - Zacchaeus Adangor, atoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Ribas, ya yi murabus daga kujerarsa ana zaune kalau.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, kwamishinan ya sanar da hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa Gwamna Siminalayi Fubara, yana mai bayyana dalili na kashin kai a matsayin babban abun da yasa ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara: Dalilin da ya sa gwamnati ta rushe ginin majalisar dokokin jihar Rivers

Rikicin siyasar Ribas ya dauki sabon salo
Rikicin Wike da Fubara Ya Dauki Sabon Salo Yayin da Atoni Janar na Ribas Ya Yi Murabus Hoto: John Nwaokorie, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ma ta rahoto ci gaban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu da ke da masaniya kan halin da Adangor ke ciki sun bayyana cewa murabus din nasa ya samo asali ne daga damuwa kan yadda aka gudanar da shirin gabatar da kasafin kudin ba bisa ka’ida ba.

Har ila yau, an kuma rahoto cewa Adangor ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda gwamnan Ribas ya gabatar da kasafin kudin ga yan majalisar biyar kacal.

Bugu da kari, an tattaro cewa rusa majalisar dokokin jihar da aka yi a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, ya taka rawar gani a shawarar da ya yanke na yin murabus.

Rikicin siyasa: Dan majalisar Ribas ya magantu

A wani labarin kuma, mun ji cewa Tonye Adoki, daya daga cikin jiga-jigan ƴan majalisar dokokin Rivers da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP kwanan nan ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya koma tsohuwar jam’iyyarsa.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gobara ta kama ofishin gwamnan jihar Borno

Idan dai za a iya tunawa Adoki da wasu mambobi 26 na majalisar mai wakilai 32 sun sanar da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba.

Sun bayyana rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ne dalilin da ya sa suka ɗauki matakin komawa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng