“Ainahin Dalilin da Yasa Muka Tsige Gwamna da Yan Majalisar PDP 16”: Alkalin Kotun Daukaka Kara
- Alkalin Kotun Daukaka Kara Mai shari'a Abdulaziz Waziri ya ce an tsige yan majalisar PDP a Filato ne saboda jam'iyyar bata da tsari a lokacin da aka zabi yan takarar
- Mai sahri'a Waziri ya ce zaben yan takara duk abu ne da ya shafi kafin zabe da bayan zabe, ya danganta da yanayinsu
- Kotun Daukaka Karar ta tsige Gwamna Caleb Mutfwang, sanatoci uku da yan majalisar wakilai duk bisa wannan dalili
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Yola, Adamawa - Mai shari'a Abdulaziz Waziri na Kotun Daukaka Kara ya yi bayani kan hukuncin kotun da ya tsige Gwamna Caleb Mutfwang da majalisun tarayya da na jiha na PDP a jihar Filato.
Alkalin wanda ya magantu a makon bangaren shari’a na shekarar 2023 a Yola, babban birnin jihar Adamawa, a ranar Talata, 12 ga watan Disamba, ya ce wadanda ke sukar hukuncin kotun ba su fahimci abun ba, inji rahoton The Nation.
Ya jaddada cewar PDP bata da tsarin jam'iyya a daidai lokacin da suka gabatar da yan takararsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkalin ya jaddada cewar yana cikin mambobin kwamitin da suka yanke hukunci a shari'ar, shari'ar da aka yi da PDP a jihar Filato ba batu ne na kafin zabe ba. Ya bukaci jama'a da su tsaya a bangaren doka a kodayaushe.
Dalilin da ya sa aka kori gwamnan Filato, Sanatoci, yan majalisar wakilai na PDP da sauransu
Ku tuna cewa kotun daukaka kara ta tsige Gwamna Caleb Mutfwang, wanda kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Filato ta tabbatar da zabensa a baya, kan hujjar cewa PDP bata da tsari a lokacin da aka zabe shi a jam'iyyar.
Hakan ce ta kasance da sanatoci uku da yan majalisar wakilai da aka zaba a inuwar PDP a jihar Filato.
An kuma kori yan majalisar dokokin jihar Filato 16 saboda wannan dalili.
Mai shari’a Waziri ya bayyana dalilin da ya sa aka kori yan majalisar PDP
Mai shari’a Waziri ya ce:
“Wasu mutane na iya cewa abu ne na kafin zabe, an yarda. A kan batun cancanta, zabe na iya zama al'amuran kafin da kuma bayan zabe ya danganta da abin da za ku iya fahimta a matsayin cancanta. Batun jihar Filato ba batun kafin zabe ba ne kamar yadda ake cewa.
“Akwai wani umarni da babbar kotun jihar Filato ta bayar cewa PDP ta je ta yi taronta a wannan ranar. Sun yi watsi da umarnin kotun, sun daukaka kara zuwa kotun daukaka kara, za su iya soke hukuncin da karamar kotun ta yanke, sun shigar da kara a kotun koli, sun kasa ci gaba da daukaka karar kuma kotun koli ta yi watsi da karar.
"Saboda haka, yadda lamarin yake a wancan lokaci shine cewa ba su da tsari a kasa. Don haka, duk dan takarar da suka cike bai da hurumi a idon doka, don haka abun da ya faru kenan."
Masu takarar kujerar Lalong
A wani labarin, mun ji cewa a kwanakin nan Lalong ya ce bai yanke shawara ba kan ci gaba da zama a matsayin Minista ko kuma Sanata a Najeriya.
Lalong dai ya yi nasara a Kotun Koli bayan ya samu mukamin Minista a gwamnatin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng