Jam’iyyar LP Ta Umurci Peter Obi Ya Ba Tinubu Hakuri? Gaskiya Ta Bayyana
- An yi ikirari a dandalin sadawar Facebook cewa jam'iyyar LP tana fushi da Peter Obi
- Mawallafan labarin sun yi ikirarin cewa jam'iyyar LP ta umurci Obi da ya ba Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu hakuri a hukumance
- Legit Hausa ta tuna cewa Obi ya yi takara da Tinubu a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2023 amma ya sha kaye tare da zuwa na uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Wani rahoto da ke yawo a dandalin Facebook ya yi ikirarin cewa jam'iyyar LP ta umurci dan takararta na shugaban kasa a zaben watan Fabrairun 2023, Peter Obi, da ya ba Shugaban kasa Bola Tinubu hakuri.
Rahoton ya yi ikirarin cewa Obi ya yi “karyar da ba ta dace ba” a kan Shugaban kasa Tinubu.
Ku yi watsi da ikirarin karya game da LP da Obi
Ya kuma bayyana cewa Obi na fuskantar barazanar kora daga jam'iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"LP ta umurci Obi da ya ba Shugaban kasa Tinubu hakuri kan karyar ganganci ko ya fuskanci kora daga jam'iyyar."
Ana iya ganin rubutun na Facebook a nan da nan.
Amma da gaske ne cewa LP ta bukaci Obi ya bayar da hakuri da barazanar kora? Wani dandalin binciken kwakwaf, Africa Check ya gudanar da bincike.
Bisa wani rikicin cikin gida a jam'iyyar LP, ana fafutukar shugabanci tsakanin bangarorin jam'iyyar biyu: bangaren da Julius Abure ke jagoranta da bangaren da Lamidi Apapa ke jagoranta. Sai dai kuma, Abure ne Obi da shugaban jam'iyyar adawar na kasa suka sani.
Kafafen watsa labarai a Najeriya sun rahoto cewa bangaren Apapa sun zargi Obi da yiwa Najeriya suka mai illa. Wannan bangare na ta nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu.
Sai dai kuma dandalin bincike kwakwaf ya ce wani bincike da aka yi a shafin LP na yanar gizo da soshiyal midiya bai nuna sanarwar ba.
Haka kuma babu wani rahoto kan haka daga gidajen jaridu abun dogaro, duba ga matsayin Obi.
Africa Check ta ce ta tuntubi LP kan zargin ba da umurnin amma bata samu amsa ba a daidai lokacin kawo rahoton nan.
Jigon APC ya yi hasashen makomar Tinubu
A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC a yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya gargadi Shugaba Tinubu kan yadda ya ke tafiyar da mulki.
Lukman ya ce jam’iyyar za ta iya rasa madafun iko idan ba a kawo karshen halin kunci da ‘yan kasar ke ciki ba, cewar Tribune.
Asali: Legit.ng