Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin ICPC, FCSC da Wasu Mutum 11 a Villa

Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin ICPC, FCSC da Wasu Mutum 11 a Villa

  • Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC), Musa Adamu a Aso Villa ranar Laraba
  • Bayan haka shugaban ya kuma baiwa sabon shugaban hukumar ma'aikata (FCSC) da mambobin hukumar 11 rantsuwar kama aiki
  • Hakan ya gudana ne a wani ɗan biki da aka shirya jim kaɗan gabanin fara taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Musa Adamu a matsayin sabon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC) ta ƙasa.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin ICPC da FCCS a Villa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya rantsar da sabon shugaban ICPC ne a wani ɗan kwarya-kwaryan biki da aka shirya a ɗakin taron fadar shugaban ƙasa jim kaɗan kafin shiga zaman majalisar zartarwa (FEC) ranar Laraba.

Kara karanta wannan

IPPIS: Shugaba Tinubu ya sauya matakin da Buhari ya ɗauka kan jami'o'i da wasu manyan makarantu

Channels tv ta ce bayan haka Shugaban Kasa ya kuma rantsar da sabon shugaban hukumar kula da ma'aikatan FG, Farfesa Tunji Olaopa da kuma mambobin hukumar guda 11.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taƙaitaccen bayani kan sabbin shugabannin biyu

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya karanta a wurin, ya yi taƙaitaccen bayanin sabbin shugabannin ICPC da FCSC.

A cewarsa, sabon shugaban ICPC, Musa Adamu, ya yi aiki a matsayin Antoni Janar kuma ministan shari'a a jihar Jigawa tsakanin 2019 zuwa 2023.

Ya kuma bayyana cewa shugaban FCSC da ya kama aiki ya fito ne daga jihar Oyo kuma malamin makaranta ne sannan tsohon babban sakatare ne.

Mista Ngelale ya ce Farfesa Olaopa yana da kwarewa a harkar koyarwa a jami'a kuma ya yi aiki a matsayin babban sakatare a ma'aikatu biyar, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake ofisoshi akalla 17 a sakateriyar ƙaramar hukuma 1 a jihar Kano

Gwamnan APC Ya Nada Sabbin Hadimai Sama da 150

A wani rahoton na daban kun ji cewa Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya naɗa sabbin masu taimaka masa na musamman guda 162.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Yinka Oyebode, ya fitar ya ce waɗanda aka naɗa zasu fara aiki ranar 1 ga watan Janairu, 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel