Atiku Ya Magantu Kan Kin Sakin Bayanan Karatunsa, Ya Dauki Zafi

Atiku Ya Magantu Kan Kin Sakin Bayanan Karatunsa, Ya Dauki Zafi

  • An zargi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, da kin sakin bayanan karatunsa
  • Atiku ya yi kokarin ganin an tsige Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta hanyar tura lauyoyi don karbo bayanan karatun shugaban Najeriyan a jami'ar Jihar Chicago ta karfi da yaji
  • Jaridar Premium Times ta bukaci samun bayanan karatun Atiku, ciki harda na digirinsa na biyu, amma ya ki sakinsu bayan makonni da dama; yanzu ya yi martani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya ce wata jaridar Najeriya ba ta da hurumin gudanar da bincike a kan bayanansa da ya ce ba su da wata takaddama ko abun boyewa.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashi wata 6 a gidan kaso saboda satar maggi da sabulu, Alkali ya ba shi zabi

Ku tuna cewa jaridar ta rahoto cewa Atiku ya ki sakin bayanan karatunsa, duk da cewar a shekarar nan ne ya tura lauyyinsa Amurka don tilastawa Jami'ar Jihar Chicago (CSU) sakin bayanan karatun Shugaban kasa Bola Tinubu.

Atiku ya magantu kan bayanan karatunsa
Atiku Ya Magantu Kan Kin Sakin Bayanan Karatunsa, Ya Dauki Zafi Hoto: George Osodi
Asali: Getty Images

Bayanan karatu: Atiku ya dau zafi

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben watan Fabrairun 2023, ya zargi jaridar da makirci da rashin sanin makamar aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yi ikirarin cewa an shirya labarin ne.

Atiku ya ce:

“Tsarin aikin jarida na neman tabbatar da gaskiya ne a lokacin da aka samu sabani a kai ko kuma ana kokarin yin rufa-rufa da gangan kan abu na ra'ayin jama'a.
"Abun da Premium Times ta yi a kan wannan lamari babu ko daya daga cikin wadannan ka’idoji guda biyu. Labarin da Premium Times ta yi magana akai ba komai ba ne face farauta- kuma ma mara tushe balle makama."

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Kungiyar CAN ta yi martani game da harin bam kan masu Maulidi a Kaduna, ta tura bukata

A halin da ake ciki, jaridar na nan kan rahoton ta sannan ta jaddada cewar Atiku ya yi watsi da bukatarta na neman ya saki bayanan karatunsa tsawon fiye da watanni biyu.

Atiku ya ziyarci makarantarsa ta firamare

A wani labarin, mun ji cewa dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar ya ziyarci makarantarsa ta firamare a Jada, jihar Adamawa a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wallafar da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) inda ya bi sa da hotuna da bidiyoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel