Jigon APC Ya Bayyana Abu 1 Tak da Zai Jawo Wa Tinubu Faduwa a 2027, Ya Ba da Shawara

Jigon APC Ya Bayyana Abu 1 Tak da Zai Jawo Wa Tinubu Faduwa a 2027, Ya Ba da Shawara

  • Jigon jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Salihu Lukman ya sake gargadin jam’iyyar kan irin mulkjin da ta ke yi a kasar
  • Tsohon shugaban jam’iyyar ya ce idan ba a yi abin da ya dace ba za a iya rasa madafun iko a kasar kamar yadda PDP ta yi a 2015
  • Lukman ya bayyana haka ne a yau Laraba 13 ga watan Disamba a Abuja yayin shirye-shiryen kaddamar da littafinsa na siyasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban jam’iyyar APC a yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya gargadi Shugaba Tinubu kan yadda ya ke tafiyar da mulki.

Lukman ya ce jam’iyyar za ta iya rasa madafun iko idan ba a kawo karshen halin kunci da ‘yan kasar ke ciki ba, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya aikawa irinsu Atiku sako, ya fadi wanda za a tsaida takara a 2027

Jigon APC ya gargadi jam'iyyar game da zaben 2027, ya ce komai na iya faruwa
Jigon APC, Lukman Salihu ya caccaki tsarin mulkin jam'iyyar. Hoto: Bola Tinubu, Salihu Lukman.
Asali: Facebook

Mene jigon APC ke cewa kan jam'iyyar?

Jigon APC ya ce akwai alaka mai tsami tsakanin masu mulki da talakawan kasa wanda hakan zai yi tasiri a 2027, cewar Daily Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon darakta janar na APC ya bayyana haka ne a yau Laraba 13 ga watan Disamba a Abuja yayin shirye-shiryen kaddamar da littafinsa.

Ya ce:

“Ya kamata mu fada wa kan mu gaskiya, dimukradiyya ba ta samar da abin da ake nema ba, amma shugabanni ba su damu da hakan ba.
“Abin na neman wuce gona da iri, za mu iya fuskantar bore daga jama’a a 2027 da kuma rasa madafun iko.
“Idan ana son kauce wa wannan dole a kawo karshen wahlhalun da ake ciki, za mu iya rasa gwamnati a koma kamar 2015.”

Wane gargadi jigon APC ya yi?

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Abin da Ya Taimaki Tinubu Kan Amaechi, Osinbajo da Lawan Inji Jagoran APC

Lukman ya ce dole hakkin mu ne mu fada wa shugabanni gaskiya musamman Shugaba Bola Tinubu.

Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar ke cikin wani irin mawuyalin hali na tsadar rayuwa wanda har yanzu babu wasu kwararan matakai kan hakan.

Tinubu ya sake saka baki a rikicin Ondo

A wani labarin, Shugaba Tinubu a karo na biyu ya sake shiga rikicin jihar Ondo don kawo karshenta.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya sasanta rikicin a kwanakin baya amma a banza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.