Shari’ar Kano: An Ja Kunnen Tinubu Yayin da Malamai 500 Suka Rokawa Abba Nasara a Kotu
- ‘Ya ‘yan jam’iyyar NNPP suna so Bola Ahmed Tinubu ya guji katsalandan a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano
- Shugabannin NNPP sun tara malamai da ake tunanin sun kai 500 domin yin addu’o’in samun nasara a kotun koli
- Kotun koli ce za ta raba gardama tsakanin jam’iyyar APC da Abba Kabir Yusuf a kan shari’ar gwamnan a zaben 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Jam’iyyar NNPP ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu cewa ka da ya tsoma bakinsa a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.
The Guardian ta ce shugabannin jam’iyyar NNPP na yankin Arewa maso yamma sun shirya taron addu’o’i na malamai kimanin 500.
NNPP tana so Tinubu ya cire hannunsa
A wajen taron ne mataimakin shugaban NNPP na shiyyar, Shehu M. Bello ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya bar kotu tayi aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehun Garu ya ce tashin hankalin da ake neman jawowa a jihar Kano a dalilin hukuncin kotun daukaka kara da na korafin zabe ne.
"Mutane sun san wadanda su ka zaba kuma sun gamsu da sakamakon zaben da ak ayi.
Abba Kabir Yusuf ya yi nasara. Muna sauraron hukuncin kotun koli. Mu na kira ga mutanenmu su zauna lafiya."
- Shehu M. Bello
'Yan NNPP sun yi kira ga kotun koli
‘Dan siyasar ya ce sun yi addu’o’i ne domin ganin Gwamna Abba Yusuf ya yi nasara kotu.
This Day ta rahoto cewa sakataren gudunarwa na NNPP, Bala Yunusa Muhammad yana kira ga Alkalan kotun kolin kasar su yi adalci.
Bala Yunusa Muhammad ya roki babban kotun kasar ta tabbatar da zabin al’umma a Kano a maimakon a biyewa abin duniya a shari'ar.
An yi wa Abba addu'a a Enugu
Legit Hausa ta samu labari wasu masoya da magoya bayan Kwankwasiyya sun yi addu’o’in nasarar NNPP a shari'ar har a jihar Enugu.
Aliyu Adamu Kwankwaso ya jagoranci salloli da karatun Al-Kur’ani da aka yi saboda kotun koli ta bar Abba Kabir Yusuf a karagar mulki.
Majiyarmu ta ce an yi taron addu'o'in ne a Garken Shanu da ke Awkwunanu a Enugu.
Binciken jami'an gwamnati a Kano
An samu labari cewa ‘yan sandan jihar Kano sun kama Abubakar Gambo, Baba Yahaya da Nuhu Mansir inda ake yin bincike a kan su.
Ana tuhumar wadannan mutane da yin takardun bogi domin samun damar yin gwanjon kayan gwamnati ba tare da izinin kwamishina ba.
Asali: Legit.ng