Gwamnan PDP da Ke Fuskantar Barazanar Tsigewa ya Saka Labule da Majalisar Zartarwa, Bayanai Sun Fito
- Yayin da Gwamna Fubara na jihar Rivers ke cikin tashin hankali na yiyuwar tsige shi, ya shiga ganawar sirri da majalisar zartarwa a jihar
- A yau ne 'yan majalisun jihar 27 daga cikin 32 su ka sauya sheka zuwa APC daga PDP yayin da ke tsaka da rikicin siyasa a jihar
- Gwamna Fubara na ganawar gaggawar ce a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Port Harcourt a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya shiga ganawar gaggawa da majalisar zartarwa na jihar.
Ganawar gaggawar na zuwa ne bayan 'yan majalisu 27 daga 32 sun sauya sheka zuwa APC daga PDP, Legit ta tattaro.
Mene dalilin rikicin siyasa a Rivers?
Jaridar The Nation ta tattaro cewa ganawar na gudana ne a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Port Harcourt a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan majalisun da su ka bar PDP, an gano su da tutar jam'iyyar APC bayan zaman majalisar.
Ana zargin Ministan Abuja Nyesom Wike da haddasa husuma a jihar tun bayan samun matsala da Gwamna Fubara na jihar.
'Yan majalisu nawa su ka sauya sheka zuwa APC?
'Yan majalisar guda 27 na biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike wadanda yanzu ya ke rike da Minista a gwamnatin APC.
Wike shi ne ya kawo Fubara a matsayin wanda ya tsayar a takarar gwamnan jihar wanda ya yi nasara a zaben.
Tun farkon hawanshi mulki, Fubara da mai gidansa su ka fara samun matsala a tsakaninsu kan wasu dalilai da dama a tsakaninsu.
'Yan majalisa 27 sun koma APC a Rivers
A wani labarin, a yau Litinin 11 ga watan Disamba, wasu 'yan majalisar jihar Rivers sun sauya sheka zuwa APC daya PDP.
Jihar Rivers na da 'yan majalisu 32 yayin da 27 daga cikinsu su ka sauya sheka da safiyar yau Litinin bayan zaman majalisar a birnin Port Harcourt.
Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasa ke kara ƙamari a jihar tun farkon hawan gwamnan karagar mulki.
Asali: Legit.ng