Cikin Gwamnan PDP Ya Duri Ruwa Yayin da Yan Majalisar PDP 27 Suka Sauya Sheka Zuwa APC

Cikin Gwamnan PDP Ya Duri Ruwa Yayin da Yan Majalisar PDP 27 Suka Sauya Sheka Zuwa APC

  • Rikicin siyasar da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike ya sake ɗaukar sabon salo
  • Hakan na zuwa ne yayin da ƴan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike suka fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Ƴan majalisar su 27 sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar ta PDP ne zuwa APC a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Majalisar dokokin jihar Rivers ta samu gagarumin sauyi yayin da mafi yawancin ƴan majalisar suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Ƴan majalisar dokokin masu biyayya ga Wike sun sauya sheƙa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne a safiyar yau Litinin, 11 ga watan Disamba, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun kashe mutum 3

Yan majalisar dokokin Rivers 27 sun koma APc
An samu sauyin sheka a majalisar dokokin jihar Rivers Hoto: @OfficialAPCNg, @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Mambobi 27 ne na majalisar suka sanar da sauya sheƙar ta su, lamarin da ya haifar da wani sabon salo na rikicin siyasa tsakanin Gwamna Similanayi Fubara da ubangidansa, Nyesom Wike, wanda shi ne ministan babban birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan majalisar PDP sun koma APC

Sanarwar sauya sheƙar tasu ta faru ne a farfajiyar majalisar yayin zaman majalisar na ranar Litinin, rahoton TheCable ya tabbatar.

Majalisar dokokin jihar ta Rivers dai tana da jimillar ƴan majalisu 32 ne.

Wannan yana nuna cewa ƴan majalisar masu biyayya ga Wike a yanzu suna da rinjaye fiye da kashi biyu bisa uku domin tsige Gwamna Siminalayi Fubara

Ƙudirin gyaran ƙananan hukumomin jihar Rivers na shekarar 2023 shi ma ya tsallake karatu na biyu a zaman majalisar na yau.

Ƴan majalisa 27 sun juya wa Fubara baya

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya bayyana gaskiya kan shirin haɗa maja da Kwankwaso da wasu jam'iyyu 6

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana cewa ƴan majalisar dokokin jihar 27 sun sanya ƙafar wando ɗaya da Gwamna Siminalayi Fubara.

Hakan na zuwa ne dai yayin da ake cigaba da shirye-shiryen tsige gwamnan daga kan kujerarsa, biyo bayan saɓanin da ya samu da Wike.

Malamin Addini Ya Shawarci Wike da Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin Jehovah Eye Salvation, Fasto Godwin Ikuru, ya shawarci Wike kan rikicinsa da Gwamna Siminalayi Fubara.

Fasto Ikuru ya buƙaci tsohon gwamnan na jihar Rivers da ya ɗaga wa gwamnan ƙafa ya bar shi ya gudanar mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng