Jam’iyyar APC Ta Fatattaki Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Niger, Ta Fadi Dalili
- Jam'iyyar APC ta dakatarb da shugaban karamar hukumar Suleja da ke jihar Niger kan zargin rashin da'a da cin zarafin ofishinsa.
- Jam'iyyar ta dakatar da shugaban karamar hukumar na tsawon watanni uku, yayin da ta nada mataimakinsa matsayin shugaban riko
- APC ta kuma zargin shugaban jam'iyyar da kunna wutar rikici a gunduar Kurmi-Sarki, wanda a cewar ta dakatarwar za ta kawo ci gaba a jam'iyyar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Niger - Kwamitin gudanar da aiki na jam'iyyar APC a jihar Niger ya dakatar da shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Suleja, Gambo Ibrahim.
Jam'iyyar ta dakatar da Ibrahim na tsawon watanni uku kan zargin rashin da'a da wuce gona da iri a aikinsa.
Sakataren riko na jam'iyyar na jihar, Alhaji Shuaibu Isah ya sanar da hakan a cikin takardar dakatarwar mai kwanan wata 7 ga watan Disamba, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya sa aka kori shugaban karamar hukumar?
Alhaji Isah ya ce:
"Ana zargin Gambo Ibrahim da kin bin dokokin da suka kafa gudanarwar jam'iyyar, da kuma kin rarraba kudi ko kyaututtuka idan jam'iyyar ta umurce shi.
"Haka zalika akwai rikicin da aka yi a gundumar Kurmi-Sarki, wanda aka gano da sa hannun shugaban karamar hukumar, don haka korarsa za ta kawo ci gaba a jam'iyyar."
Sakataren jam'iyyar ya kuma bayyana cewa kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya dakatar da shugaban karamar hukumar na tsawon watanni uku.
Haka zalika ya umurci mataimakin shugaban karamar hukumar da ya zama shugaban riko har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Ba wannan ne karon farko ba, ko a shekarar 2020, Channels TV ta taba ruwaito yadda jam'iyyar APC ta dakatar da wani shugaban karamar hukumar kan zargin cin hanci da rashawa.
CBN zai rufe Opay, Moniepoint da sauran bankunan 'online'?
A wani labarin, hadimin Shugaba Tinubu ta fuskar kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, ya karyata rahoton cewa CBN zai rufe bankunan 'online' irin su Opay, Kuda, Moniepoint, da sauransu.
A makon da ya gabata babban bankin Najeriya ya ba bankunan ajiyar kudi (DMBs) umurnin rufe duk wani asusun ajiyar kudi da ba shi da BVN da NIN daga shekara mai zuwa, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng