Saboda Abdul Samad BUA da Wasu, an Tilasta Ganduje Dakatar da Babban Taron APC

Saboda Abdul Samad BUA da Wasu, an Tilasta Ganduje Dakatar da Babban Taron APC

  • Majalisar zartaswar jam'iyyar APC ta yanke shawarar dakatar da babban taron kaddamar da kwamitoci biyar da ta shirya yi a Abuja
  • Wani rahoto ya gano cewa jam'iyyar ta dakatar da taron ne biyo bayan tutsun da ta sha daga dan kasuwa Abdul Samad BUA da wasu mutane
  • Shugaban rukunin kamfanonin BUA an ruwaito ya ki amincewa da tayin jam'iyyar na shiga kwamitin kudi na jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC), ta dage babban taronta na kaddamar da manyan kwamitocin gudanarwar jam'iyyar har sai nan gaba.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa jam'iyyar ta dage taron ne biyo bayan kin amincewar Abdul Samad Rabiu, mai kamfanin BUA na shiga kwamitin kudi na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Majalissar Tarayya ta shirya taron jin ra’ayin jama’a kan kasafin kudin 2024

Abdul Samad/Ganduje/APC
Jam'iyyar APC ta dakatar da taron da ta shirya gudanarwa na kaddamar da wasu manyan kwamitoci biyo bayan wani cikas da ta samu. Hoto: BUAgroup/Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

A ranar Litinin, kakakin jam'iyyar Felix Morka ya sanar da cewa kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa ya kafa kwamitoci guda biyar don gudanarwar jam'iyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su waye a kwamitin kudi na jam'iyyar APC?

Kwamitocin sun hada da kwamitin kudi, watsa labarai, magance rikicin cikin gida da kwamitin da zai kula da harkokin jam'iyyar da gwamnati

Jam'iyyar ta sanya sunan Uguru Ofoke matsayin shugaban kwamitin kudi, yayin da Bashir Gume ya zama sakatare, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Sauran mambobin sun hada da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio; kakakin majalisar tarayya, Abbas Tajudeen; ministan kudi, kodinetan ministan tattalin arziki.

Sauran sun hada da Wake Edun da kuma babban dan kasuwar man fetur A.A. Rano, da dai sauransu.

Matsayar APC kan taron kaddamar da kwamitocin

Baya ga Rabiu, wanda ya ki amincewa ya zama mamba a kwamitocin na mutum 34, akwai wasu mambobin kwamitin da suka tayar da jijiyoyin wuya kan rashin tuntubarsu kafin saka sunansu a kwamitocin.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno PDP yayin da Atiku da fitaccen gwamna suke neman iko, karin bayani

Da ya ke jawabi jim kadan bayan taron majalisar zartaswar jam'iyyar a jiya Litinin, Morka ya ce an cimma matsaya na dakatar da kaddamar da kwamitoci har sai baba-ta-gani, Leadership ta ruwaito.

A wani bangaren, kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya yi Allah wadai da harin da aka kai gidan baturen zabe na jihar Kogi, Dr. Gabriel Longpet, tare da yin kira ga jami'an tsaro da su kamo da hukunta wadanda suka aika hakan.

Tinubu ya magantu kan kisan masu maulidi

A wani labarin na daban, Shugaba Tinubu ya bayar da umurnin yin bincike biyo bayan wani harin bam da rundunar soji ta kai kan wasu masu maulidi a Kaduna, Legit ta ruwaito.

Shugaban kasar ya kuma umurci a bai wa wadanda suka tsira daga harin duk wata kulawa da suke bukata ta asibiti yayin da ake bincike kan lamarin

Asali: Legit.ng

Online view pixel