Rikicin gida: Jam’iyyar PDP ta rantsar da shugabannin rikon kwarya na Yankin Arewa

Rikicin gida: Jam’iyyar PDP ta rantsar da shugabannin rikon kwarya na Yankin Arewa

- PDP ta rantsar da shugabannin rikon kwarya na yankin Arewa maso yamma

- Jam’iyyar ta kafa kwamitin riko ne bayan ta gagara gudanar da zabe a baya

- Majalisar NWC ta ce ‘Yan kwamitin rikon kwaryan za su yi aiki na kwana 40

Jaridar This Day ta ce majalisar NWC ta jam’iyyar hamayya ta PDP ta nada kwamitin rikon kwarya da za su kula da yankin Arewa ta yamma.

A ranar Litinin, 19 ga watan Afrilu, 2021, aka rantsar da shugabannin riko da za su rike ragamar jam’iyyar adawa ta PDP a Arewa maso yamma.

NWC ta nada shugabannin rikon kwarya ne a sakamakon matsalar da aka samu wajen gudanar da zaben shugabanni na yankin a kwanakin baya.

KU KARANTA: Zaben PDP ya jawo cacar baki tsakanin Kwankwaso da Gwamnan Sokoto

Sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya bada wannan sanarwa inda ya ce NWC ta dauki wannan mataki ne a madadin NEC.

Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta dogara da sashe na 29(2)(b) na dokar jam’iyya da ya bada damar a nada kwamitin riko.

Shugaban kwamitin shi ne Dr. Aminu Abdullahi, sauran ‘ya ‘yansa sun hada da; Alhaji Sani Baba, Hon. Ali Madaki, da Hon. Ibrahim Lawal Dankaba.

Ragowar su ne: Hon. Umaru Maye, Alhaji Akibu Dalhatu, A’isha Ibrahim Madina, Hamza Yunusa da Alhaji Baba Kasim Ibrahim a matsayin sakatare.

KU KARANTA: Kwankwaso, Tambuwal da ‘Yan siyasan da za su gwabza a 2023

Rikicin gida: Jam’iyyar PDP ta rantsar da shugabannin rikon kwarya na Yankin Arewa
Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus
Asali: Twitter

Da yake jawabi, Ologbondiyan ya bayyana cewa sababbin shugabannin za su jagoranci al’amurar jam’iyyar PDP na lokacin da bai zarce kwanaki 40 ba.

Majalisar NWC ta yi kira ga shugabannin rikon kwaryar su yi aiki da doka wajen sauke nauyinsu.

Jam’iyyar PDP ta yi kira ga ‘ya ‘yanta da duka sauran masu-ta-cewa da ke jihohin Arewa maso gabas su cigaba da aiki tare domin ganin an kai ga nasara.

A jiya ne ku ka ji cewa uwargidar gwamnan Kaduna, Hadiza El-Rufai ta ci gyaran nahawun jam'iyyar PDP a takardar sanar da dakatar da Rabiu Kwankwaso.

Mai dakin Gwamnan jihar Kaduna ta nuna yadda sanarwar da aka fitar ta ke ciki da tulin kura-kurai. Hadiza El-Rufai ta zakulo kuskure kusan 40 a takardar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel