Dan Majalisar NNPP Ya Magantu Kan Zargin Maja da PDP da Sauransu Don Kayar da Tinubu da APC a 2027
- Dan majalisar wakilai na jam'iyyar NNPP, Abdulmumin Jibrin, ya yi watsi da rade-radin maja da PDP da sauran jam'iyyun siyasa
- Jibrin ya ce babu kamshin gaskiya a rade-radin yana mai bayyana shi a matsayin aikin makirai kuma wanda ya kamata a yi watsi da shi
- Sai dai kuma, ya bayyana cewa NNPP a shirye take ta yi maja da APC mai mulki da sauran jam'iyyu a kasar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya yi martani a kan zargin maja da jam'iyyar PDP.
Jubrin ya ce jam'iyyar NNPP bata tattaunawa da PDP ko wata jam'iyyar siyasa a yanzu haka.
A wata sanarwa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @AbdulAbmJ, ya bayyana rahoton yin maja da PDP a matsayin kanzon kurege da aikin makirai wanda ya kamata a yi watsi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, dan majalisar na NNPP, ya ce a shirye jam'iyyar take ta tattauna da jam'iyyar APC, PDP, LP ko sauran jam'iyyun siyasa a kasar.
Ya ce:
“An ja hankalinmu zuwa ga wani sako da ake yadawa a wasu sashi na kafafen yada labarai cewa babbar jam’iyyarmu, NNPP na tattaunawa da PDP da sauran jam’iyyu domin yiwuwar yin hadaka.
“Babu kamshin gaskiya a cikin wannan. Karya ce karara. Jam’iyyarmu ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayinta cewa kofa a bude take na hadin gwiwa, kawance da hadewa da APC, PDP, LP da kowace jam’iyyar siyasa.
“A halin yanzu babu wata magana da ke gudana kuma jam’iyyar ba ta halarci kowani taro don tattaunawar hadaka ko maja da PDP ko wata jam’iyya ba. Wannan aiki ne na makirai kuma ya kamata a yi watsi da shi."
SDP ta karyata batun maja da jam'iyyun adawa
A wani labari makamancin wannan, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa, a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba, jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta yi watsi da rade-radin yin hadaka da wasu jam'iyyun adawa don raba Shugaban kasa Bola Tinubu da kujerarsa.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Alfa Mohammed, kakakin kungiyar, ya bayyana cewa "jam'iyyar SDP ta kuduri aniyar yin hulda mai kyau da gwamnatin Tinubu na tsawon shekaru uku masu zuwa."
Asali: Legit.ng