Sanatan Kano Ya Bayyana Gaskiyar Zaman Abba 'Dan NNPP Kafin Hukuncin Kotun Koli

Sanatan Kano Ya Bayyana Gaskiyar Zaman Abba 'Dan NNPP Kafin Hukuncin Kotun Koli

  • Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila yana tunanin nasarar APC a kotu ba za ta sa NNPP ta rasa mulkin jihar Kano
  • Sanatan Kano ta kudu ya ce fatansu shi ne Alkalan kotun koli su tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf ya lashe zaben 2023
  • Sumaila ya musanya ikirarin cewa an saba doka wajen tsaida Abba, ya ce gwamnan cikakken ‘dan jam’iyya ne

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A wata hira ta musamman da aka yi da shi, an bijirowa Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila maganar shari’ar gwamnan Kano.

Sanata Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila mai wakiltar Kudancin Kano a majalisa ya fadawa Daily Trust suna fatan nasara a kotun koli.

Abdulrahman Kawu Sumaila
Sanatan NNPP, Abdulrahman Kawu Sumaila Hoto: Musaa Yaa'u Musaa
Asali: Facebook

Jam'iyyar NNPP ta girgiza da tsige Abba a Kano

Kara karanta wannan

Neman karbe kujerar Abba Gida-Gida a kotu zalunci ne kawai, Malamin Musulunci

A matsayinsa na jagora na jam’iyyar NNPP, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce hukuncin da aka yanke a kotu baya sam ba su yi dadi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, ‘dan majalisar dattawan yana ganin Alkalan kotun koli za su ruguza nasarar APC, a tabbatar da gwamna Abba Kabir Yusuf a mulki.

Akwai masu ra’ayin cewa tun da kotun korafin zabe da na daukaka kara ta tsige Abba, zai yi wahala ya kai labari, amma Sumaila bai cikinsu.

Abba v Gawuna Akwai dama a kotun koli - Sumaila

"Wannan ba gaskiya ba ne. Duba abin da ya faru a Osun. Ina sa ran nasara a Kotun koli; kuma na yi imani za su yi mana adalci.
Akwai shari’o’i kusan 50 da hukunci da aka yi a kotun koli cewa lamarin zama ‘dan jam’iyya batu ne da ake yi kafin a shiga zabe.

Kara karanta wannan

"Muna Fatan Nasara": Hadimin Abba Ya Magantu Yayin Da Kotun Koli Ke Shirin Fara Zama Kan Shari'ar Kano

Ni ba lauya ba ne, amma akwai shari’o’i da dama irin wannan. Abba ya shigo jam’iyyar NNPP kusan kwanaki 40 kafin in shigo."

- Abdulrahman Kawu Sumaila

An soki hukuncin zaben Gwamnan Kano

Sumaila ya nuna bai so ya yi magana a kan shari’ar da ake yi a kotu, duk da masu fashin baki da nazarin al’amura suna tofa albarkacin bakinsu.

‘Dan siyasar ya ce ana da damar yin tir da yadda aka tsige gwamnatin NNPP musamman bayan rudanin da aka samu kan takardun CTC.

An rahoto Kawu Sumaila yana cewa Abba Kabiru Yusuf ya saye fam, ya lashe zabe, kuma INEC ta tabbatar da sunan shi yadda doka ta tanada.

“Mutanenmu ba su son rashin adalci. Idan kuma ana tunanin sai an karbe Kano saboda zaben 2027, mutane na jira, ba ayi wa jama’a dole.
Dole ‘yan siyasa mu fahimci akwai farko da iyaka a komai, a girmama zabin mutane."

Kara karanta wannan

Ba kuskure ba ne: Ahmad Gumi ya dauki zafi a kan kisan masu taron Maulidi a Kaduna

- Abdulrahman Kawu Sumaila

Abba ya yi nade-naden mukamai a Kano

Abba Kabir Yusuf ya kawo karshen rade-radin da ke yawo game da Dr. Abdullahi Baffa Bichi a Jihar Kano, ya sanar da cewa SSG bai da lafiya.

Gwamna ya umarci shugaban ma’aikatan gwamnatin Kano, Abdullahi Musa, ya lura da ofishin sakataren gwamnatin kafin ya dawo daga waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng