Kano: Sabon Rikici Ya Barke a Kotu Tsakanin Lauyoyin Abba da Alkalan Kotu Kan Fitar da Takardun CTC
- An kaure a kotun daukaka kara tsakanin lauyoyin Abba Kabir da alkalan kotun kan fitar da takardun CTC da ke nuna nasarar Abba
- Lauyoyin gwamnan sun isa kotun ne don daukaka kara inda su ka nemi a sauya hukuncin da ya ba su rashin nasara
- Wannan na zuwa ne bayan fitar da takardun CTC da kotun ta yi wanda ke nuna cewa Abba Kabir ne ya yi nasara a shari'ar zaben
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Rikici ya sake barkewa yayin da lauyoyin Gwamna Abba Kabir suka je daukaka kara a kotu.
Layoyin gwamnan sun samu wata ‘yar hatsaniya da alkalan kotun bayan fitar da takardun CTC da ke tabbatar da nasarar Abba Kabir, Legit ta tattaro.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/72cc408013aa5569.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Kungiyar Arewa ta bayyana hukuncin da ya kamata Kotun Koli ta yanke a shari'ar jihar Kano
![Rikici ya kaure tsakanin lauyoyin Gwamna Abba Kabir da alkalan kotun daukaka kara Rikici ya kaure tsakanin lauyoyin Gwamna Abba Kabir da alkalan kotun daukaka kara](https://cdn.legit.ng/images/1120/adefb29f2e1d9078.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
Mene ya jawo sabon rikicin?
Sabon rikicin ya barke ne bayan dukkan bangarorin sun ki amincewa da juna kan takardun CTC da kotun ta fitar a jiya, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyoyin Gwamna Abba Kabir sun kai korafi na daukaka kara a Abuja inda su ke neman adalci a hukunci da aka yi a kuskure.
Har ila yau, alkalan kotun daukaka karar sun ki amincewa da bukatarsu a kotun inda hakan ya tilasta lauyoyin zuwa kotun shiyya da ke Kano.
Har ila yau, alkalan kotun sun tura takarda ga lauyoyin don gyaran kura-kurai a takardun CTC wanda lauyoyin Abba Kabir su ka ki.
Wane hukunci kotun ta yanke?
A ranar Juma'a ce 17 ga watan Nuwamba gamayyar alkalan guda uku su ka sake rusa zaben Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/32234048f1b231a7.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Abba Vs Gawuna: 'Yan sanda sun roki malaman addini su dage da yin wa'azi kan tada tarzoma a Kano
Kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a, Moore Adumein ta rusa zaben kan zargin cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ba dan jam'iyyar NNPP ba ne.
Amma a takardun CTC, kotun ta yi watsi da hukuncin karamar kotun inda ta umarci biyan Abba Kabir naira miliyan daya.
Jam'iyyar NNPP ta yi martani kan takardun CTC
A wani labarin, Jami'yyar NNPP ta yi martani kan shari'ar zaben gwamnan Kano bayan fitar da takardun CTC.
NNPP ta ce abin takaici ne yadda Najeriya ta zubar da mutuncinta musamman a bangaren shari'a.
Ta yi zargin da nufi aka yi saboda rashin fitar da takardun da wuri ganin cewa mai daukaka kara ya na kwanaki 14 ne kacal.
Asali: Legit.ng