Kungiyar Arewa Ta Bayyana Hukuncin Da Ya Kamata Kotun Koli Ta Yanke a Shari'ar Jihar Kano

Kungiyar Arewa Ta Bayyana Hukuncin Da Ya Kamata Kotun Koli Ta Yanke a Shari'ar Jihar Kano

  • Kungiya Arewacin Najeriya, 'Northern Initiative for Peace and Economic Development' ta bukaci a yi hukuncin adalci a shari'ar Kano
  • Kungiyar ta kiran ne ganin yadda jama'ar jihar Kano su ka fito kwansu da kwarkwata su ka zabi Gwamna Abba Kabir a jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli tsakanin Gwamna Abba Kabir da Nasiru Gawuna a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiya a Arewacin Najeriya ta bukaci Kotun Koli ta yi watsi da hukuncin Kotun Daukaka Kara a jihar Kano.

Hakan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli tsakanin Abba Kabir da kuma Nasiru Gawuna a jihar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

An fada ma kotun koli wanda za ta sanar ya ci zabe tsakanin PDP da APC a Filato

Kungiyar Arewa ta fadi abin da ya kamata Kotun Koli ta yi a shari'ar Kano
Kungiyar a Arewa ta roki Kotun Koli kan hukuncin zaben jihar Kano. Hoto: Abba Kabir, Nasiru Gawuna.
Asali: Facebook

Wane martani kungiyar ta yi kan shari'ar Kano?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Abel Jilemsam ya fitar a ranar Laraba 6 ga watan Disamba a Jos da ke jihar Plateau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abel ya ce hukuncin Kotun Zabe da na Kotun Daukaka Kara duk akwai kuskure a ciki ganin cewa anyi fatali da zabin al'umma.

Vanguard ta tattaro Abel na cewa:

"Jama'ar jihar Kano sun fita don zaben Abba Kabir kuma dole a mutunta su da kuma jin kukansu.

Wane shawara kungiyar ta bayar a shari'ar Kano?

"Juya wannan sakamakon zaben ba iya ruguza martabar dimukradiyya za ta yi ba har ma da cire wa mutane aminci kan zabubbuka.
"Mu na kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da kuma bangaren shari'a da su yi hukuncin adalci a shari'ar da ake yi."

Kara karanta wannan

Zanga-zanga ta barke a Kudancin Najeriya kan hukuncin zaben Kano, sun tura sako ga Tinubu

Abel ya kara da cewa hakan shi zai kara wa mutane kwarin gwiwa yayin ake dakon hukuncin Kotun Koli baya hukuncin kananan kotuna.

Abba Kabir ya sha kaye a kotu

A wani labarin, kotu ta rufe asusun bankunan gwamnatin jihar Kano guda 24 saboda rusau a jihar.

Tun bayan hawan Gwamna Abba Kabir ya ke rushe-rushe inda ya ce an yi gine-gine ba bisa ka'ida ba a jihar.

Kungiyoyin 'yan kasuwa da masu shaguna sun maka gwamnan a kotu don kwatar hakkinsu na lalata musu dukiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.