Asirin APC Ya Fara Bankada Bayan Kama Jigon Jami'yyar da Zargin Siyan Kuri’u a Zaben Shugaban Kasa

Asirin APC Ya Fara Bankada Bayan Kama Jigon Jami'yyar da Zargin Siyan Kuri’u a Zaben Shugaban Kasa

  • Kotun ta garkame wani jigon APC kan zargin siyan kuri’u a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu
  • Kotun da ke zamnata a Ikeja da ke Legas ta garkame wanda ake zargin ne mai suna Wahad Hammed
  • Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi ne a kotun kan zarge-zarge guda biyu na hadin baki da kuma cin hanci

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – Babbar kotu da ke zamanta a jihar Legas ta garkame jigon jam’iyyar APC kan zargin siyan kuri’u.

Wanda ake zargin mai suna Wahab Hammed ya tabbatar da siyan kuri’un a zaben da aka gudanar na wannan shekara.

Asirin APC ya fara tonuwa bayan kama shi jigonta da siyan kuri'u zaben shugaban kasar
An kama jigon APC kan zargin siyan kuri'u a zaben shugaban kasa. Hoto: Ganduje Umar, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene ake zargin jigon APC da aikatawa?

Kara karanta wannan

Ba a gama da shari'ar zabe ba, Kotu ta rufe asusun bankunan gwamnatin Kano 24 kan dalili 1 tak

Dan siyasar zai ci gaba da zama a hannun hukumar EFCC har bayan hukumar ta gama bincikenta kafin mika shi ga kotun don yin hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta gurfanar da shi ne a kotun kan zarge-zarge guda biyu na hadin baki da kuma cin hanci da rashawa, cewar Leadership News.

An fassara tuhumar da ake masa cikin harshen Yarbanci bayan wanda ake zargin ya ce ba zai iya magana da Turanci ba.

Mai gabatar da kara na hukumar EFCC, Samuel Daji tun farko ya fada wa kotun cewa Hammed sun hada baki da Ijitola don siyan kuri’un.

Wane mataki kotun ta dauka kan jigon APC?

Sai dai har yanzu ba a san inda Ijitola ya ke ba bayan sun sayi kuri’un a ranar zaben shugaban kasa da ‘yan Majalisun Tarayya, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kasafin Tinubu ya fusata Arewa, ba a ware sisi domin aikin wutan Mambilla a 2024 ba

Daji ya ce wanda ake zargin ya aikata hakan ne a rumfa ta 28 a mazabar makarantar mata ta Gbaja da ke Surukere a jihar.

Ya kara da cewa aikata laifin ya sabawa dokar kasa sashi na 121 cikin baka 1 da kuma 121 cikin baka na 5 a kundin tsarin zabe.

Lauyan wanda ake zargi, Olabiyi Ademola ya bukaci kotun ta bar Hammed a hannun EFCC tun da za a kammala binciken a karshen makon nan.

Kotu ta yi hukunci kan rusau a Kano

A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan rusau da Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya aikata a jihar.

Kotun ta rufe asusun bankunan gwamnatin jihar guda 24 da kuma biyan tara na diyyar biliyan 30 ga wadanda ke kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.