Sukar Gwamnatin Tinubu Ta Jawo Kashim Shettima Ya Yi wa Peter Obi Tsirara a Siyasa

Sukar Gwamnatin Tinubu Ta Jawo Kashim Shettima Ya Yi wa Peter Obi Tsirara a Siyasa

  • Fadar Shugaban Kasa ta maida martani inda aka yi kakkausan raddi a kan Peter Obi da ya yi takara a LP
  • Hakan ya biyo bayan yadda ‘dan adawan ya dauki lokaci mai tsawo yana ta sukar gwamnatin Bola Tinubu
  • A wani jawabi da aka fitar, Kashim Shettima ya ce tsohon gwamnan yana kokarin yaudarar magoya baya ne

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Fadar shugaban kasa ta dauki lokaci ta maida martani ga Peter Obi a kan sukar da yake yi wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Raddin ya fito daga ofishin Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ta bakin kakakinsa, Stanley Nkwocha a Twitter a ranar Talata.

Kashim Shettima, Peter Obi
Kashim Shettima da Peter Obi Hoto: Kashim Shettima, Peter Obi
Asali: Twitter

Mai magana da yawun Mataimakin shugaban kasar ya zargi ‘dan takaran na 2023 da bata gwamnatin Bola Tinubu saboda haushin fadi zabe.

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Biya Diyyar Mutane 85 da Sojoji Su Ka Kashe da Bam a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya ce Peter Obi yaudara yake yi

Peter Obi ya soki gwamnatin tarayya a kan kudin da aka kashe wajen zuwa taron COP28 da shirin gyara gidan mataimakin shugaban kasa.

Stanley Nkwocha ya ce Obi ya yi amfani da zargin zuwa taron COP28 da mutane 1411 ne saboda cin ma manufar siyasa ta hanyar yaudara.

Idan shugaban kasa ya wanke kan shi daga zargi, sai ‘dan takaran na LP ya sake dauko wani batu, hakan ya jawo aka yi masa dogon martani.

Hadimin mataimakin shugaban kasar ya ce ‘dan takaran na LP ya shafe awanni 24 wajen sukar gwamnatin Bola Tinubu, don haka ya yi raddi.

Jawabin Stanley Nkwocha a kan Peter Obi

"Ya zama dole a bayyana gaskiyar lamari. A sukar da ya yi wa Tinubu da Kashim Shettima, ya na kokarin nuna shi kadai ya damu da ‘Yan Najeriya

Kara karanta wannan

Maulidi: Atiku ya yi martani kan harin bam da aka yi kan bayin Allah a Kaduna, ya ba da shawara

Amma da an zare mayafin za a gano cewa har yanzu yana jin haushin fadi zaben 2023 ne."

-Stanley Nkwocha

Gyaran gidan da Kashim Shettima zai zauna

Nkwocha a jawabinsa ya yi bayanin yadda Goodluck Jonathan ya fara bada kwangilar gyaran gidan mataimakin shugaban kasa tun 2010.

Kamar yadda Obi ya nemi karasa kwangilolin da aka bar su da yake gwamna a Anambra, jawabin ya ce haka ake so a kammala wannan aikin.

A jawabin sai da aka jefi tsohon gwamnan da zargin bada kwangilolin titi na N30bn a lokacin da ya fahimci wa’adinsa ya zo karshe a jihar Anambra.

Obi, Kwankwaso da Atiku a 2027

Kwanaki aka ji labari Atiku Abubakar ya fara kiran ‘yan adawa irinsu Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su yi wa jam’iyyar APC taron dangi a 2027.

Babu mamaki Peter Obi zai goyi bayan shirin, amma NNPP ta ce Rabiu Kwankwaso za a ba tuta idan har an dunkule domin tunkarar Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng