Kano: Ana Son Hukunta Abba Ne Don 2027, Masu Zanga-zanga a Abuja Sun Fusata, Sun Ba da Misali
- Daruruwan masu zanga-zanga ne su ka cika birnin Abuja don kalubalantar hukuncin shari'ar zaben jihar Kano
- Masu zanga-zangar sun fito daga ko wane bangare na kasar inda su ka nuna rashin jin dadinsu da abin da aka yi a jihar Kano
- Wani matashi daga jihar Akwa Ibom ya ce dole ya fito zanga-zangar saboda watarana hakan zai iya faruwa a jiharsa
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Dandazon jama'a na ci gaba da zanga-zanga a birnin Tarayya, Abuja kan hukuncin shari'ar jihar Kano.
Masu zanga-zangar sun kuma nuna rashin jin dadinsu da hukuncin jihohin Zamfara da Plateau har ma da jihar Nasarawa.
Wane gargadi masu zanga-zangar su ka yi?
Har ila yau, sun gargadi mahukunta da su kiyayi kawo cikas a kujerar Abba Kabir na jihar Kano inda su ka bukaci adalci a shari'ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jama'a da dama na ci gaba da nuna rashin jin dadinsu musamman a hukuncin Kotun Daukaka Kara da aka yi a shari'ar jihar Kano.
Matasan sun bayyana cewa an shirya abin ne don hukunta Abba Kabir shi kadai saboda zaben 2027, cewar Tribune.
Masu zanga-zangar sun hada da mutane daga Arewacin kasar har zuwa Kudancin Najeriya da kuma mazauna yankunan Wasa da Madala a Abuja.
Mafi yawan masu zanga-zangar mata ne da suka bayyana ra'ayinsu da yarukan Hausa da Ibo da Fulani da Yarbanci.
Wane martani masu zanga-zangar ke yi?
Masu zanga-zangar sun yi hakan ne don nuna cewa kansu a hade ya ke don yaki da rashin adalci, cewar Newstral.
Wani daga cikinsu mai suna Ekwerre ya bayyana cewa ya shiga zanga-zangar ce don nuna rashin jin dadin abin da aka aikata a Kano.
Ya ce idan zai faru a Kano to wata rana zai iso jiharsa ta Akwa Ibom da kuma sauran jihohin Najeriya baki daya.
Abba Kabir ya bankado badakalar kayan tallafi
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya yi nasarar bankado wata badakala ta kayan tallafin rage radadi.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya kaddamar da kayan tallafi a kwanakin baya don tallafa wa marasa karfi a jihar.
Asali: Legit.ng