Ba Abin da Zai Hana Abba Yin 8, Jigon NNPP Ya Zargi APC Kan Sake Shigar da Kara, Ya Fadi Dalili

Ba Abin da Zai Hana Abba Yin 8, Jigon NNPP Ya Zargi APC Kan Sake Shigar da Kara, Ya Fadi Dalili

  • Yayin da ake ci gaba da dakon hukuncin Kotun Koli a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano, jigon jam’iyyar NNPP a Najeriya ya yi hasashe
  • Olufemi Ajadi ya ce jam’iyyar APC bata lokacinta ta ke wurin neman kwace kujerar Gwamna Abba Kabir a jihar Kano
  • Ajadi ya ce babu abin da zai hana Abba Kabir yin shekaru takwas a kan mulki ganin yadda al’umma ce ta zabe shi da mafi yawan kuri’u

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Jigon jam’iyyar NNPP, Ambasada Olufemi Ajadi ya ce sake shigar da kara da APC ta yi kan Abba Kabir na Kano bata lokacinta ta ke yi.

Ajadi ya bayyana haka a yau Litinin 4 ga watan Disamba a Abuja yayin ganawa da manema labarai, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sama da 200 sun shirya tsaf don tabbatar da Abba Gida-Gida ya yi nasara a kotu

Jigon NNPP ya yi martani kan kokarin na kwace mulkin Abba Kabir
Jigon NNPP ya yi martani kan sake shigar da karar APC kan Abba Kabir. Hoto: Ajadi O, Ganduje A. Abba Kabir.
Asali: Facebook

Mene jigon NNPP ke cewa kan Abba Kabir?

Ya bukaci jam’iyyar ta APC da ta gabatar da shaidar cewa Abba Kabir ya mika jabun takardu ga hukumar zabe mai zaman kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba jam’iyyar ta sake shigar kara Kotun Koli kan zargin Gwamna Abba Kabir ya mika takardun bogi ga hukumar zabe.

Olufemi ya ce wannan abin kunya ne yadda APC ke son tunbuke zabin al’ummar jihar Kano karfi da yaji, cewar Independent.

Wane hasashe Ajadi ya yi kan kujerar Abba?

Ya ce:

“Ya kamata APC ta gane cewa ba kasar shirme mu ke ba, duk yadda ta yi kokarin kwace kujerar Abba ba za ta yi nasara kan zabin al’umma ba.
“Gwamna Abba Kabir zai yi shekaru takwas a kan mulkin gwamnan jihar Kano babu tantama.

Kara karanta wannan

Ka jira ka ga makomarka tukunna, APC ta tura zazzafan gargadi ga Abba Kabir kan zargin abu 1 tak

“Ina kira ga mabobin jam’iyyar NNPP da su kwantar da hankalinsu inda ya ce su na da tabbacin samun nasara a Kotun Koli.”

Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin shari’ar zaben gwamnan jihar a Kotun Koli bayan NNPP ta daukaka kara.

APC ta tura gargadi ga Gwamna Abba Kabir

A wani labarin, Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta tura sakon gargadi ga Gwamna Abba Kabir kan kashe kudaden jihar.

APC na zargin Yusuf da amfani da kudaden jihar wurin daukar nauyin masu yin zanga-zanga don ta da zaune tsaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel