Gwamna Abba da Kwankwaso na tsaka mai wuya yayin da rikicin NNPP ya ƙara tsanani kan abu 1

Gwamna Abba da Kwankwaso na tsaka mai wuya yayin da rikicin NNPP ya ƙara tsanani kan abu 1

  • Rikicin cikin gida a jam'iyyar NNPP ya kara tsanani yayin da tsagin Kwankwaso da Major Abgo suka fara musayar yawu
  • A wata hira da yan jarida a Abuja, Major Agbo ya buƙaci jami'an tsaro sun tuhume Kwankwaso kan abubuwaɓ da ke faruwa a Kano
  • Sai dai tsagin ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a 2023 ya maida martanin cewa Agboh bai da ikon cewa komai da sunan jam'iyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya dauki sabon salo yayin da ɓangare ɗaya ya nesanta kansa daga zanga-zangar Kano.

Rikicin NNPP ya kara tsananta.
Rikici Ya Kara Mamaye NNPP Yayin da Tsagi Daya Ya Nesanta Kansa da Zanga-Zangar Kano Hoto: NNPP
Asali: UGC

Leadership ta ce tsagin ya kuma roki hukumomin tsaron Najeriya su bincike tsagin da ke goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Wasu jiga-jigan NNPP sun ƙara jefa Gwamna Abba da Kwankwaso cikin babbar matsala, gaskiya ta bayyana

Sai dai tsagin Kwankwaso ya maida martani da cewa tsagin da ke goyon bayan Dakta Major Agbo ba su da hurumin tsoma baki kan harkokin NNPP domin tuni aka kore su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon tada yamutsin da ya biyo bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige gwamnan Kano, tsagin NNPP karkashin Major Agbo ya nemi jami'an tsaro su tuhumi ɓangaren Kwankwaso.

Da yake hira da yan jarida a Abuja, Mista Agbo ya ce tada zaune tsaye da kisan kai ba ya cikin manufofin jam'iyyar NNPP, inda ya roki mazauna jihar Kano su rungumi zaman lafiya.

Major ya fallasa cewa Dipo Johnson, mai magana da yawun Kwankwaso ba dan jam’iyyar NNPP bane mai rijista kuma an dauke shi ne domin tada zanga-zanga.

Vanguard ta rahoto Agbor na cewa:

"Muna gayyatar hukumomin tsaro da su binciki Dipo Johnson da tawagarsa, domin ba su da alaka da NNPP."

Kara karanta wannan

Kaduna: Rundunar Sojin Ƙasa ta ɗauki laifi, ta faɗi gaskiyar abinda ya jawo jefa bam a taron Maulidi

Tsagin Kwankwaso ya maida martani

Da take rushe ikirarin Major Agbor, NNPP ta bayyana cewa wasu ne suka ɗauki hayar korarrun mambobin jam'iyyar domin su tozarta Gwamna Abba Kabir da Kwankwaso.

A wata sanarwa da Ladipo Johnson ya fitar a madadin NNPP ta ƙasa, ya bayyana cewa kalaman da Major Agbor ya yi ƙarya ce mara tushe balle makama.

"Muna kira ga yan Najeriya su yu watsi da waɗannan kalaman daga bakin maƙiyan Najeriya da mutanen cikinta," in ji shi.

Kotun koli ta yanke hukunci kan tsige Uzodinma

A wani rahoton na daban Kotun koli a Najeriya ta kawo karshen shari'a kan zaben gwamnan jihar Imo wanda aka yi a shekarar 2019.

Yayin yanke hukunci ranar Talata, kotun ta kori ƙarar wadda ta nemi sauke Hope Uzodinma na APC daga kujerar gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262