Daga Karshe, Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Ta Nemi Tsige Gwamnan APC

Daga Karshe, Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Ta Nemi Tsige Gwamnan APC

  • Kotun koli a Najeriya ta kawo karshen shari'a kan zaben gwamnan jihar Imo wanda aka yi a shekarar 2019
  • Yayin yanke hukunci ranar Talata, kotun ta kori ƙarar wadda ta nemi sauke Hope Uzodinma na APC daga kujerar gwamna
  • Masu shigar da karar sun nemi kotun ta kori Gwamna Uzodinma bisa hujjar cewa APC ba ta tsaida shi takara a zaɓen ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da ta nemi tsige Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kwamitin alƙalai bakwai na kotun ƙaraƙashin mai shari'a Inyang Okoro ya kori ƙarar da ta nemi a kori Uzodinma daga matsayin gwamnan Imo.

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.
Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukuncin Kan Karar Tsige Gwamna Uzodinma Na APC Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

Ƙarar ta buƙaci kotun koli ta tsige Uzodinma daga kujerar gwamna bisa hujjar cewa APC ba ta tsaida shi takara ba a zaɓen da ya lashe na zangon farko a 2019.

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya ƙara samun gagarumin goyon baya da ka iya sa ya lallasa Abba a Kotun Koli

Haka nan kuma karar ta nemi kotun ta rushe tsawon shekarun da Gwamna Uzodinma ya yi a kan madafun iko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar AA a zaben 2019, Mista Uche Nwosu, ne ya ɗaukaka ƙarar har zuwa kotun koli amma daga bisani PDP da ɗan takararta, Emeka Ihedioha, suka nemi shiga shari'ar.

Masu kara sun yi bayanin cewa idan har kotun koli ta amince da Nwosu ne ɗan takarar APC, to babu wata hujja a shari’a kan hukuncin da ta yanke na korar Ihedioha.

Don haka, PDP ta bukaci kotun koli ta maida dan takararta, Ihedioha, kan kujerar gwamnan Imo tunda APC ta tsaida ‘yan takara biyu a zaben, wanda haramun ne a doka.

Kotun koli ta yanke hukunci?

Sai dai kuma a ranar Talata 5 ga watan Disamba, 2023, kotun kolin ta ce ba ta da hurumin sauraren karar, wanda ta bayyana a matsayin rashin gaskiya da harzuka.

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

A hukuncin wanda mai shari'a Tijjani Abubakar ya karanta, kotun kolin ta bayyana cewa ƙarar ba ta cancanta ba gaba ɗaya, The Nation ta ruwaito.

Kotun kolin ta kuma ci tarar Cif Mike Ozehkome, SAN, wanda ya wakilci PDP da Ihedioha a shari'ar kudi naira miliyan 40.

Wani abin mamaki shi ne, ƙarar wadda ta shafe sama da shekaru uku a kotun koli, an tsara ci gaba da sauraronta a watan Oktoba amma daga baya aka ɗage ta.

An sake ɗage zaman sauraron ƙarar ne har sai zuwa bayan zaben gwamnan jihar Imo, wanda Gwamna Uzodinma ya sake samun nasara ranar 11 ga watan Nuwamba.

PDP ta yunkuro a jihar Ekiti

A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta fara farfaɗowa a jihar Ekiti yayin da wasu ɗaruruwan mambobi da jiga-jigan SDP suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar.

Masu sauya shekar waɗanda suka kasance magoya bayan tsohon gwamna, Segun Oni, sun rungumi PDP ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262