Zaben Gwamna: NNPP Ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara, Ta Fadi Matakin Gaba

Zaben Gwamna: NNPP Ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara, Ta Fadi Matakin Gaba

  • Yayin da aka yanke hukuncin shari'ar zaben jihar Taraba, dan takarar jam'iyyar NNPP ya garzaya Kotun Koli
  • Farfesa Sani Yahaya ya ce kwata-kwata babu adalci a cikin dukkan hukunce-hukuncen kotunan guda biyu
  • Jam'iyyar ta NNPP a jihar Kano har ila yau, ta garzaya Kotun Koli don kalubalantar shari'ar zaben jihar

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - Dan takarar jam'iyyar NNPP, Farfesa Sani Yahaya ya ki amincewa da hukuncin Kotun Daukaka Kara da aka gudanar.

Sani Yahaya ya dauki matakin garzaya wa Kotun Koli ne don kalubalantar hukuncin kotun.

Jam'iyyar NNPP ta garzaya Kotun Koli don kalubalantar shari'ar zaben gwamna
NNPP Ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara. Hoto: Professor Sani Yahaya/Facebook.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a shari'ar Taraba?

Kotun Daukaka Kara yayin hukucinta ta kori karar Farfesan saboda rashin gamsassun hujjoji a gabanta, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama a shari'ar neman tsige gwamna mai ci, ta ba da dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba wanda ke jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe.

Yayin da ya ke martani kan hukuncin, Farfesan ya ce zai daukaka kara Kotun Koli saboda kwato hakkinsa da al'umma su ka ba shi.

Yahaya ya ce babu adalci a dukkan hukuncin da aka gudanar a kotunan zaben guda biyu a baya.

Wane martani dan takarar NNPP ya yi a Taraba?

Ya ce a dukkan hukuncin kotun zabe da kuma Kotun Daukaka Kara an yi wa adalci karan tsare tare da rashin tsari, cewar Daily Post.

Wannan na zuwa ne bayan takwaranshi na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf shi ma ya garzaya Kotun Koli don kalubalantar da hukuncin kotu.

Abba ya rasa kujerarshi ta gwamna a dukkan kotunan guda biyu inda ya ce an yi tsantsar rashin adalci a hukunce-hukuncen.

Kara karanta wannan

Kano: Shin akwai alamun nasara ga Gwamna Abba da gwamnonin PDP 2 da aka rusa zabensu? An yi bayani

Yayin hukuncin kotunan, sun tabbatar da nasarar Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe.

Kotu ta yi hukunci a zaben Taraba

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Taraba.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Agbu Kefas na jam'iyyar PDP yayin da ta kori karar dan takarar jam'iyyar NNPP, Farfesa Sani Yahaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.