Rabon Mukamai Ya Sake Kawo Rarrabuwar Kai a Jam'iyyar APC

Rabon Mukamai Ya Sake Kawo Rarrabuwar Kai a Jam'iyyar APC

  • Shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Benue sun caccaki salon mulkin Gwamna Hyacinth Alia
  • Shugabannin sun zargi gwamnan da yin watsi da su a matakin da ya ɗauka na naɗa shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomin jihar
  • Shugabannin jam'iyyar na ƙananan hukumomin jihar sun kuma zargi gwamnan da ɗasa wa da ƴan adawa a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Rikicin da ke tsakanin gwamnan jihar Benue, Rabaran Hyacinth Alia, da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya ɗauki wani sabon salo.

Hakan dai na zuwa ne a yayin da shugabannin jam'iyyar a dukkanin ƙananan hukumomin jihar 23 suka nesanta kansu da naɗin shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomin da gwamnan ya yi, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka mutum 7 a wani kazamin hari da suka kai a wasu kauyuka 2

Jam'iyyar APC a Benue ta shiga rikici
Rarrabuwar kai ya barke a jam'iyyar APC a jihar Benue Hoto: Hyacinth Alia
Asali: Twitter

Shugabannin jam’iyyar sun kuma zargi gwamnan da yin watsi da jam’iyyar da yin ƙawance da jam’iyyar adawa a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya kawo rarrabuwar kai a jam'iyyar APC a Benue

Hakan dai ya bayyana ne a ranar Alhamis a sanarwar da shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomi 23 suka fitar, inda suka nuna damuwarsu kan yadda gwamnan ya yi watsi da jam’iyyar tun bayan hawansa mulki.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Misalai sun yi yawa cewa ba za a iya cewa komai ya daidaita tsakanin Gwamna Hyacinth Alia da jam’iyya a jiha da kuma ƙananan hukumomi ba."

Taron shugabannin jam’iyyar ya nuna rashin jin daɗinsa kan matakin da gwamnan ya ɗauka na rashin tuntuɓarsu a naɗin shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin da ya yi.

Sun kuma zargi gwamnan da cewa ba a samunsa kuma ba ya amsa kiran waya, da rashin sanya shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da ƙananan hukumomi wajen yin naɗin manyan muƙamai a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya aike da sako mai muhimmanci ga Wike kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Sai dai ƙungiyar ta bayyana gamsuwarta da shugabancin Akume, da shugaban ƙasa Bola Tinubu, da shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa da jiha.

Sanatan APC Ya Faɗi Laifin Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya yi magana kan bambancin da ke tsakanin gwamnatin Shugaba Tinubu da ta Muhammadu Buhari.

Ali Ndume ya bayyana cewa Shugaba Tinubu shi ne ke riƙe da aƙalar gwamnatinsa yayin da Buhari kuwa ya bari ɓarayi suka yi ta sata a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng